✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IMF ya yaba wa CBN kan manyan tsauraran manufofi da na musayar kudi

Hukumar Zartarwar Asusun  Lamuni na Duniya (IMF) ta kammala tattaunawa ta daftari na IB da ganawarsu da jami’an Babban Bankin Najeriya a watan jiya  tare…

Hukumar Zartarwar Asusun  Lamuni na Duniya (IMF) ta kammala tattaunawa ta daftari na IB da ganawarsu da jami’an Babban Bankin Najeriya a watan jiya  tare da yaba wa manyan tsare-tsaren Babban Bankin Najeriya (CBN).

Manyan Daraktocin IMF sun yaba wa murmurewar da tattalin arzikin Najeriya yake yi ta hanyar raguwar tashin farashin kayayyaki da karfafa kudin ajiyar kasar nan.

“Tashin farashin kayayyaki har yanzu babban kalubale ne ga Bankin CBN, Darktocin sun amince cewa daukar tsauraran dokokin kudi shi ne mafita. Sun karfafa gwamnati ta bunkasa yin abu a bayyane da sanar da jama’a  da bunkasa tsarin dokokin kudi wanda ya hada da yin amfani da hanyoyi da aka saba kamar tsaurara dokar kudi ko kuma ka’idojin adana kudi,” inji rahoton.

Daraktocin sun bukaci a kawo karshen shiga tsakani na kai-tsaye ga tattalin arziki da bankin yake yi don bankin ya samu damar fuskantar daidaita farashi.

Sun yaba wa shugabannin Bankin CBN  kan kokarinsu na daidaita musayar kudi tare da yaba wa karin samar da hanyoyin musayar kudi. Sun ce daidaita musayar kudi tare da samar da musayar kudi ta bai-daya za ta taimaka wa rage tashin farashin kayayyaki.

Daraktocin sun bayyana cewa soke hana musayar kudi da kuma samar da musayar kudin kasashen waje zai rage badakala da kuma bunkasa tattalin arziki.

Daraktocin sun yaba wa ragin rashin biyan bashi da bunkasa harkokin banki amma kuma sun gano cewa yi wa harkar karbar bashi garambawul da kuma sanya jari ga bankuna za ta ci gaba da yin tasiri kan harkokin kudi. Sun bayar da shawarar karfafa jari da sanya ido kan asara da sanya ido kan kadarori da kauce wa dokokin da ke da sarkakiya da bunkasa dokokin hada-hadar bankuna da suka ce hakan zai taimak kwarai da gaske. Daraktocin sun bayar da shawarar kafawa tare da iyakance jari ga bankunan da ba su da karfi.

Daraktocin sun bukaci hukumomi su aiwatar da tsarin gyaran fuska don bunkasa tattalin arziki don cimma burin kudirin bunkasa kasa. Sun ce don bunkasa hada-hadar kasuwanci, aiwatar da shirin farfado da wutar lantarki da karfafa hada-hadar kudi ta bai-daya da yin garambawul ga bangaren lafiya da bangaren ilimi da aiwatar da dokokin da za su rage bambancin jinsi suna da muhimmanci.

Darktocin sun ce akwai bukatar a karfafa harkokin gwamnati da tafiyar da ita a fili da karfafa tsare-tsaren yaki da cin hanci da suka hada da  bunkasa yin gaskiya a ma’aikatun gwamnati.

Darktocin sun yaba wa bunkasa ingancin kididdigar tattalin arziki da karfafa rage gibin da ake samu da bunkasa kudin shiga da rage talauci da hukumomi suke dauka. Daraktocin sun bukaci gwamnatoci su kara dagewa wajen kara kaimi dangane da farfado da tattalin arziki da tsarin ci gaban kasa.

Dangane da kasar baki daya, Asusun bayar da lamunin ya ce tattalin arzikin Najeriya yana farfadowa. Tattalin arzikin kasar ya karu da kashi daya da digo tara cikin dari a shekerar 2018 inda ya karu daga sifili da digo takwas cikin dari a shekarar 2017, dangane da bunkasar masana’antu da harkokin yau da kullum da tallafin abin da ya karu a harkar man fetur, da matakan da aka dauka kan musayar kudi don bunkasa harkokin ciniki zai taimaka kwarai da gaske. Tashin farashi ya ragu da kashi 11 da digo hudu cikin dari a karshen shekarar 2018, inda hakan ya nuna a faduwar farashin kayayyakin abinci da raunin bukatar masu sayen kayayyaki da dan daidaiton farashin musayar kudi da aka samu da tsaurara dokokin kudi a shekarar 2018.

Dadin dadawa kalubalen garambawul da dokokin kudi za su cigaba da kawo cikas ga ci gaba inda hakan zai yi tasiri da asarar da ka iya fuskantar kasar, da rage talauci da bunkasar raunin jarin dan’adam kamar lafiya da ilimi. Karancin kudin shiga da raunin ma’aikatun gwamnati da cigaba da iyakance musayar kudin kasashen waje  da kalubalen da bangaren bankuna ke fuskanta yana kara  sanya harkar saka jari  da sanya tattalin arziki ya  dogara ga man fetur.

Karkashin dokokin yanzu abin lurashi ne karkashin shirin na gajeren lokaci, rashin karfafa garambawul zai sanya  ci gaba ya takaita ga kashi biyu da rabi cikin dari yayin da tattalin arziki yake fuskantar takaitar karuwar samar da man fetur da karancin sake garambawul na shekaru hudu na farashin mai. Dokokin kudi sun fuskanci kalubale sannan shirin daidaita farashin musayar kudi zai taimaka wajen rage tashin farashin kayayyaki amma kuma zai ta’azzara gasa idan ba a dauki matakin daidaiton kudin da ya dace ba. Asarar hada-hadar kudi za ta ragu. Dangane da farashin mai kuwa zai iya tashi inda hakan ya samo asali daga al’amuran siyasar duniya da suka zama tamkar kadangaren-bakin-tulu. Garambawul na ba-sani- ba-sabo biyo bayan zabubbuka da aka rika yi zai iya sanya kwarin gwiwa da sanya jari musamman  ma bias la’akari da daukan matakan da suka dace. Dangane da ci bayan lamarin kuwa karin tafiyar hawainiyar da ake samu wajen aiwatar da garambawul da raguwar faduwar farashin mai da raguwar fitar da mai da karin fargabar tsaro da ka’idojin kudi masu tsauri na duniya za su iya kawo cikas ga ci gaba da tashin farashin hada-hadar kasuwanci da sanya karin matsi kan kudin ajiyar kasashen waje da musayar kudi.

Daraktocin sun bayyana bukatar samar da karin shigar kudi don rage kudin ruwa kan kudin da ake biya a kan kayayyaki. Sun yaba wa tsarin haraji na hukumomi don kara kudin mai da ya hada da dokokin haraji . Sun jaddada muhimmancin karfafa harajin cikin gida da ya hada da karin haraji da soke ladan haraji. Samar da  kudin shiga ta hanyar garambawul din kudin shigar jihohi da kuma matakan da aka dauka na bunkasa bangaren man fetur shi ma yana da muhimmanci.

Daraktocin sun bayyana muhimmanci mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci. Sun yaba wa karin zuba jari. Amma kuma sun jaddada muhimmancin zuba jari. Sun bayar da shawarar karin kudi ga bangaren lafiya da ilimi. Sun bayyana muhimmancin cire rarar man fetur yayin karfafa walwala don tabbatar da tasirinsa ga marasa galihu zai taimaka kwarai da gaske wajen rage talauci da karin kasafin kudi. Daraktocin sun bayar da shawarar karfafa hadin kai don karfafa tattala bashin gwamnati da tattala kudi.