Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima, ya ce ingantaccen ilimi da samar da aikin yi ga matasan kasar nan ne kadai za su kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita.
Ya bayyana haka ne a wajen taron goyon baya da Kungiyar Matasa Kiristoci ta Najeriya (YOWICAN), ta shirya a ranar Juma’a don mara masa baya kan kudurinsa na yin takarar Shugaban Kasa a 2023.
- NDLEA ta kama miyagun kwayoyi na N2bn da aka shigo da su daga Indiya
- Dilolin kwaya ne suka yi kokarin yi min juyin mulki – Shugaban Guinea-Bissau
Sanata Yarima ya ce dukkan matsalolin tsaron da suka addabi kasar nan na da alaka da rashin samar da ingantaccen ilimi ga ’yan kasa, musamman ma matasa.
“Za mu samar da ilimi kyauta ga duk wani yaro tun daga matakin Firamare har zuwa kammala sakandare, babu yaron da za mu bari ba yare da ya samu ilimi ba,” cewar Yarima.
Kazalika, tsohon Gwamnan ya ce da zarar ya dare kujerar shugabancin kasar nan zai tabbatar da cewar matasa sun amfani mulkinsa fiye da kowa.
Da aka tambaye shi game da batun bayar da dama ga kowane dan kasa wajen yin addininsa, Yarima ya ce Kundin Tsarin Mulki ya ba wa kowa damar gudanar da addininsa ba tare sa tsangwama ba.
Ya kuma koka kan yadda ya ce ana amfani da addini wajen raba kan mutane don cimma bukatar kashin kai ta ’yan siyasa.
“Amma mu za mu ba wa kowa dama, duk mabiya addinin Kirista sun san irin damar da muka ba su lokacin da muka mulki Jihar Zamfara.”
Da ya ke nasa jawabin shugaban YOWICAN, Rabaran Simon Dole, ya ce kungiyar karkashin jagororinta da ke Jihohin Arewa 19 da Abuja sun shirya mara masa baya don zama zababben Shugaban Kasa a 2023.
“Shugabanni da dama sun shugabanci Najeriya amma har yanzu babu abin da ya sauya, don haka ya kamata mu gwada mutane masu riko da addini,” inji Rabaran Simon.