✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan wutar lantarki ta wadata dimbin ayyuka za su wadata – Alhaji Abbagana

Aminiya: Me za ka ce game da wannan ziyarar gani da ido da hukumarku take yi? Mu biyar muka zo wannan aiki don ganin an…

Aminiya: Me za ka ce game da wannan ziyarar gani da ido da hukumarku take yi?

Mu biyar muka zo wannan aiki don ganin an cimma kudirin gwamnati na samar da wutar lantarki don jama’a da kamfanoni su ci moriyar haka don habaka kasar nan.
Aminiya: Mene ne matsalolin da ke dabaibaye samar da wutar lantarki?
Matsala ce karama domin ya kamata a kara fahimtar juna tsakanin hukumar gwamnati mai tura wutar wato TCN da kamfanin samar da wutar da ke rarrabawa ga jihohin Kano, Jigawa da Katsina (KEDCO) don sanin lokacin da wuta ta wadata a kara tura wa jama’a. Domin kafin a sayar da kamfanin a dunkule suke waje guda.
Aminiya: Yaya za ka bayyana aikin kamfanin  KEDCO?
 A ganina suna kokari domin sun karbi kamfanin ne a watan Nuwamban bara. Kuma kamfanin a da ya shekara 40 ba wani takamaiman ka’idar aiki.  Zai dan dauki lokaci kafin a ci moriyar wannan aiki, amma kuma muna fatan su kara mayar da hankali don samar da lantarki a koyaushe.
Aminiya: Ko za ka yi karin bayani?
Samarwa da raba mita mai kati wato iya-kudinka-iya-shagalinka don magance shan wutar lantarki ba biya har guda dubu 90. Muna fatan kowace shekara za su samar da guda dubu 100. Kuma a farkon sherakar nan za su fara rabawa.
Aminiya: Ta yaya talaka zai ci moriyar wannan?
Burin gwamnati a samar da lantarki don masu sana’o’i su karu, mata masu sana’o’i a cikin gida su bunkasa sannan kamfanoni su karu kuma su dauki karin ma’aikata. Idan wutar lantarki ta wadata, ayyuka za su wadata.