✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahim Shu’aibu: Wanzamin da ke yi wa Larabawa kaciya da kaho a Saudiyya

Wani mai sana’ar wanzanci a birnin Makka da ke kasar Saudiyya mai suna Ibrahim Shu’aibu Haruna ya ce yana yi wa ’ya’yan Larabawa kaciya da…

Wani mai sana’ar wanzanci a birnin Makka da ke kasar Saudiyya mai suna Ibrahim Shu’aibu Haruna ya ce yana yi wa ’ya’yan Larabawa kaciya da kuma kaho, inda ladan da suke ba shi ya sanya rayuwarsa ta sauya.

Ibrahim dan kimanin shekara 37 dan asalin kasar Nijar ya bayyana wa Aminiya cewa Larabawa suna mutukar kaunar wanzamai a kasar Saudiyya.
Ya ce: “Babu abin da zan ce dangane da sana’ar wanzancin da nake yi, sai dai na gode wa Allah, don sana’ar ta sauya rayuwata ta hanyar samar mini da kudin shiga mai yawa da kara dankon zumunci tsakanina da bakake ’yan uwana da kuma Larabawa. Larabawa da yawa suna gayyata ta ina yi wa ’ya’yansu kaciya in cire musu hakkin wuya, ko in yi musu aski da kaho, kuma idan na gama su yi mini babbar kyauta.
“Gaskiya na gode wa Allah saboda na samu rufin asiri a sana’ata, da ita nake daukar dawainiyar iyalina har ma na taimaka wa ’yan uwa da abokan arziki.” Inji shi
Ibrahim wanda iyayensa suka haifa a Saudiyya ya bayyana cewa babbar matsalar da yake fuskanta ita ce barazana daga jami’an tsaro na kasar.
Ya ce: “Ka san a nan magana ce ta takarda, idan ba ka da ita, to babu shakka kana cikin matsala, kuma hankalinka ba zai kwanta ba, domin kullum kana fargabar kada a kama ka a sanya a gidan kaso ko a mayar da kai gida. Ko ni da nake da takardar zama a Saudiyya ba ni da tabbas, domin babu ruwansu ko kana da takardar za su iya kama ka su daure ka wata shida, daga bisani a mayar da kai kasarku. Ka ga ke nan babu tabbas. Haka muke ta gwagwarmaya muna ta bugawa da su.”
Ya ce shi ya sa da sun ga jami’an hukuma masu kame ko waye suke yi wa aski sai su gudu don kada a kama su a mayar da su kasarsu.
A ganinsa bambancin sana’ar wanzanci a Nijar da Saudiya shi ne an fi samun kudi masu yawa a Saudiyya.
“A nan za ka iya yi wa Balarabe kaho ya ba ka kwatankwacin Naira dubu ishirin na Nijar ko na Najeriya. Ka ga akwai bambanci sosai. A Nijar ko Najeriya waye za ka yi wa kaho ya ba ka dubu daya ma? Ka ga ko da gwamna ko dan majalisa ka yi wa kaho ko aski iyakacin kyautar da zai iya yi maka idan ka yi sa’a ya ba ka dubu biyar. A nan kuwa talaka ne zai ba ka makudan kudi. Shi ya sa ka ga muna makalewa a komai wulakanci da takura mana da suke yi’. In ji shi
Ya bayyana cewa mahaifinsa ne ya koya masa sana’ar a Saudiyya kuma tare da shi suke fita.