✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumomin gwamnati da kashe kudi ba izini

Babu wani bayani ga jama’a cewa Akanta Janar da Odita Janar na Tarayya sun koka kan yawan ko sababbiya ko gazawa wajen kai kudaden shiga…

Babu wani bayani ga jama’a cewa Akanta Janar da Odita Janar na Tarayya sun koka kan yawan ko sababbiya ko gazawa wajen kai kudaden shiga zuwa asusun gwamnati. Kuma wannan abin damuwa ne. Saboda wannan gazawa wasu kwamitoci na Majalisar Tarayya da wasu kadan a Majalisar Dattawa ne a wasu lokuta suke bankado rashin bin ka’ida a bangaren kudi su sanar da jama’a.
Baya ga mugun gazawar Kamfanin Mai na kasa (NNPC) na gaza kai irin wadannan kudaden shiga asusun gwamnati ko bayyana yadda aka kashe su, an gano hukumomin gwamnati fiye da 40 da kwamitin Majalisar Tarayya ya samu da irin wannan laifi, game da abin da ya shaf Asusun Tarayya da Asusun Tattara Kudin Shiga. Dokar Kula da Tafiyar da Kudi ta nuna hanyoyin karba da kashe irin wadannan kudade. Kuma Dokar Kashe Kudade ta tsara yadda za a tsare amanar albarkatun kasa da tabbatar da daidaituwar tattalin arziki na dogon lokaci da samar da cikakken rikon amana a wajen tafiyar da dukiyar kasa, kuma an lura cewa an keta karfafawa da tabbatar da bin manufofin tattalin arziki.
Misalin irin wannan keta ka’ida da ta fito fili a ’yan kwanakin nan ita ce Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta tara kudin shiga Naira biliyan 104 a shekara uku da suka gabata, amma ta kashe da dama ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ta kasa ba. Jami’an Hukumar FAAN sun yi kokarin kare keta tsarin mulkin ta bayyana cewa dimbin kudin a kashe su a bara ne a “zamanantar da filayen jiragen sama,” da tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama Stella Oduah wacce aka sallama a watan jiya ta bullo da shi. Hukumar FAAN ta fada cikin rukunin hukumomin gwamnati da ba a sanya su cikin kasafin kudin shekara-shekara da ake yi, kuma suke samo kudin kashewarsu daga kudin shigar da suka tara shigar da wani bangare cikin asusun gwamnati. Sai dai duk da haka doka ta bukaci su nemi amincewar majalisar dokoki kafin su kashe kudi mai yawa, musamman wajen gudanar da manyan ayyuka. Hukumar FAAN ta yi ikirari a takardar tuhumar da Kwamitin Majalisar Tarayya kan Kudi ya aike mata cewa ta keta dokoki wajen gaza kai kudaden shiga asusun gwamnati a shekarar 2011 da 2012.
Misalin abin da Kamfanin NNPC da Hukumar FAAN suka yi ya nuna irin yadda hukumomin gwamnati suka kai wajen kashe kudaden jama’a ba tare da izinin wadanda suka kamata ba. A fili yake cewa matsalar FAAN ya saba wa doka ce da ya auku a lokacin da ake nuna matukar damuwa kan yadda uwar ma’aikatarsu ke kekketa dokokin kashe kudi da kashe kudade ba tare da an yi kasafinsu ba. Tsarin ka’idojin kudi ya bukaci FAAN ta mika kashi 25 cikin 100 na daukacin kudin da ta samu a shekara ga asusun gwamnati. Bambancin da ke tsakanin Naira biliyan 57 da FAAN ta kasafta a matsayin kudin shiga daga gudanar da ayyukanta da Naira biliyan 17 da ofishin kasafi ya yi kiyasi ya tabbatar da rashin gaskiyaa bangaren kudin. A fili ya nuna kasafi ya daina zama ma’auni na harkar kudi na gaskiya, sai dai tabargaza da maimaita sake karkade tsohon adadin baya.
Idan kowace hukuma za ta rika fantsama ga kashe kudin da ba a kasafta ba, asusun gwamnati na iya fuskantar zama fanko, kuma aikin sanya ido na majalisa zai zamo ba ya da amfani. Matsalar da ake fuskanta ita ce kowace hukuma tana da sashin karbar kudaden shiga. Kuma bayyanar hanyar tattara bayanai na zamani zai iya sa kasar nan ta yi gyara zuwa ga wani sabon fasali da zai amfane ta sosai kamar yadda yake a baya, inda daukacin kudaden shiga na gwamnati ake sanya shi a asusu daya da sashin baitul mali ke kula da shi, kuma a ajiye rasidan baitul mali a hukumomin da abin ya shafa. Ma’aikatar Kudi ta yanzu ba ta aikin wajne ganowa da bayyana yadda ake zurare kudin shigar gwamnati da wasu ke yi da gangan ko ta haramtacciyar hanya, har sai wani ko wata kungiya ko hukuma ta fallasa, kamar yadda kasar nan take gani a ’yan makonnin nan. Wajibi ne a canja wannan.  Dokokin da suke tsara ka’idojin karbar kudaden shiga da kashe kudade tilas ne a bi su sau da kafa, in ba haka ba yanayin bala’in da ake ciki inda masu almundahana ke samun damar zuke kudaden shigar gwamnati zai iya jefa tattalin arzikin kasar nan a cikin babbar matsala. Jami’an hukumomin gwamnati da aka samu da hannu wajen karya wadancan dokoki wajibi ne a hukunta su kamar yadda doka ta tanada. Wajibi ne Akanta Janar da Odita Janar na Tarayya su mike tsaye wajen tabbatar da an yi haka.