Shugaba Muhammadu Buhari ya ware Naira biliyan 226 ga hukumomin Gwamnatin Tarayya da ake shirin rusawa, wata biyu bayan ya bukaci a waiwayi rahoton Kwamitin Steve Orosanye, wanda ya ba da shawarar rushe su.
Domin kuwa, binciken Aminiya ya gano an ware wa hukumomin da rahoton ya ba da shawarar a shafe su kudi Naira biliyan N226 a kasafin 2023.
- Sauya shekar Mustapha Inuwa zuwa PDP cin amana ne —APC
- Fursunoni 8 ne sun mutu, 57 sun jikkata a gobarar gidan yarin Iran
39 daga cikin hukumomin da lamarin ya shafa an ware musu kason biliyoyin Naira don ci gaba da gudanar da harkokinsu.
Da alamu aiwatar da rahoton Kwamitin nan na Steve Oronsaye na sake fasalin ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya ba zai tabbata nan kusa ba.
A shekarar 2011 tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya kafa kwamiti karkahin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Steve Oronsaye, tare da dora masa alhakin duba yiwuwar sake wa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati fasali.
Bayan kammala aikinsaa, kwamitin ya mika rahotonsa a 2012, inda ya ba da shawarwa narkar da wasu ma’aikatu da hukumomi cikin wasu, shafe wasunsu da kuma sauya fasalin wasu.
Sai dai kwamitin da gwamnati ta kafa don duba rahoton da kwamitin Oronsaye ya mika mata ya ki amincewa da yawa ncin shawarwarin kwamitin.
Sai kuma a 2021 gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kafa wasu kwamitoci guda biyu domin nazarin rahoton kwamitin.
Daya daga cikin kwamitocin, karkashin Alhaji Bukar Goni, gudan kuma karkashin Amal Pepple, inda suka kammala aikinsu tare da mika rahotonsu a 2022.
Bayan haka, gwamnati ta sake kafa wani kwamitin a karkashin jagorancin Ebele Okeke, don nazarin rahotannin kwamitoci biyun da ta karba don fitar da sakamako daya.
Daga nan, a ranar 19 ga Agusta, 2022, Shugaba Buhari ya ba da umarni kan a dauko rahoton kwamitin Oronsaye a sake dubawa don gwamnati ta yi amfani da shawarwarin da ke cikinsa.
Buhari ya ce an kusa kammala duba rahoton, tare sa cewa aiwatar da shawarwarin rahoton zai taimaka wajen samar da canje-canje masu amfani ga aikin gwamnati.
Buhari ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabancin manyan ma’aikatan gwamnati a fadarsa da ke Abuja, kamar yadda mai bai shi shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina, ya bayyana.