✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar zabe ta busa usur din shekarar 2015

A ranar Juma`ar makon da ya gabata ne, Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, ta busa usur akan shirye-shiryen zabubbukan shekarar 2015,…

A ranar Juma`ar makon da ya gabata ne, Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, ta busa usur akan shirye-shiryen zabubbukan shekarar 2015, wato  badi kenan idan Allah Ya kaimu. A bisa ga tsarin jadawalin zaben, da zai fara aiki daga ranar 04-10-14, wato a wannan shekarar zuwa 28-02-15. Jadawalin zaben da ya tanadi tun daga ranar 04-10-14, su bude bayar da Fom ga dukkan `yan takararsu da suke son shiga neman takarar kowane irin mukami, kama ya mayar da Fom don shiga takarar da tantancewa da musanya wadanda ba su iya tsallake siradin tsayawa zaben ba, da ranar fara yakin neman zabe da dai sauransu, kamar yadda kundin tsarin gudanar da zabubbuka da aka yi wa gyara na shekarar 2010, ya tanada a sassa daban-daban.
Babban batun da ya fi daukar hankalin `yan kasa a cikin jadawalin gudanar da zabubbukan, shi ne na ranakun da za a gudanar da zabubbukan. Zabubbukan da sashi na 25, na kundin zaben da ya tanadi a gudanar da zabubbuka kwanaki 30 zuwa 150, cikar wa`adin wadanda ke kan karagar mulki. Wata daga cikin hikimar yin hakan ita ce a samu a karkare da dukkan shari`un zabe kafin ranar rantsar da wadanda suka yi nasara, wadda a kasar nan take 29 ga watan Mayun shekarar zabubbukan. La`akari da wannan tanadi ya sanya Hukumar zaben ta tsayar da ranar 14-02-15, ta zama ranar gabatar da zabubbukan shugaban kasa da na `yan Majalisun Dokoki na kasa. Zabubbukan gwamnoni da na `yan Majalisun Dokoki na jihohi za su biyo bayan makonni biyu, wato a ranar 28-02-15.
Sakataren Hukumar zaben mai zaman kanta na kasa Augusta Ogakwu, shi ya bayyana wadannan tsare-tsare,a karshen makon jiya a Abuja, bayan wani taron kwanaki hudu a Kaduna na Kwamishinonin kasa da na jihohi da sauran manyan makarraban hukumar da Shugaban Hukumar na kasa Farfesa Attahiru Jega ya jagoranta a makon jiyan. Ya kuma fadi cewa kafin akai ga zabubbukan kasar, hukumar ta tanadi ranar 26 ga watan Yunin bana ta zama ranar da za ta gudanar da zaben Gwamnan Jihar Ekiti da kuma ranar 30 ga watan Agustar bana dai, ta zama ranar da za a gudanar da zaben Gwamnan Jihar Osun, in Allah Ya kaimu.
A wata hira da ya yi da wani gidan Radiyo da ke Kaduna, shugaban Hukumar zaben mai zaman kanta na kasa Farfesa Attahir Jega, ya fadi cewa don samun nasarar zabubbukan ne, ya sanya nan gaba kadan Hukumar za ta fara aikin rijistar masu kada kuri`a, katin da ya ce a wannan karon zai zama mai ingancin gaske da ka iya daukar shekaru 10 ana amfani da shi, katin da ya ce na din-din-din ne, saboda ingancinsa, ya yi kuma fatan su fara raba katuttukan kafin nan da zabubbukan jihohin Ekiti da Osun.
Wani muhimmin batu da Hukumar zaben mai zaman kanta ta yi begen tabbatuwarsa kafin zabubbukan badin, shi ne na gyaran Kundin zabubbukan da Farfesa Jega, ya ce tuni suka mika shi gaban Majalisun Dokoki na kasa da fatan za su amince da yi masa kwaskwarimar, watanni shidda kafin lokacin babban zaben kasar.
daya daga cikin sassan da suke so a gyara, koma a cire shi gaba daya, shi ne sashi na 31, da ya yi tanadin lallai hukumar zabe ta karbi kowane suna da jam`iyya ta ba ta a zaman dan takararta, alhali inji Farfesa Jega akan samu matsalolin a wani lokaci, na wani bai shiga takara ba, wani kuma zai iya kasancewa ba  ma shi ya ci zaben ba. Ya ce hakan sam-sam bai dace da mulkin dimokuradiyya ba, ya kuma ce tanadin hakan ya ci karo da sashi na 87, na dokar zaben da ya tanadi lallai kowace jam`iyya ta gudanar da zaben fidda gwani na cikin gida.
Tun zuwan Farfesa Jega Hukumar zaben ta kasa a shekarar 2010, `yan adawa da sauran `yan kasa suke ta fatar samun sahihin zabe, amma ka iya cewa har yanzu hakarsu ba ta cimma ruwa ba, bisa ga la`akari da zabubbukan kasa nashekarar 2011, da ya fara gudanarwa, da wadanda suka biyo baya irin na jihohin Sakkwato da Adamawa da Anambra da dai sauransu, al`amarin da yake zama tamfar ciwon ajali gwamma jiya da yau, zaben baya-bayannan shi ne na mikamin Gwamnan Jihar Anambara da aka yi a watan Nuwamban bara, zaben da aka samu wani babban jami`in Hukumar dumu-dumu da hannu cikin yin magudinsa, magudin da shi kansa Farfesa Jega ya tabbatar da faruwarsa, sannan kuma ya yi alkawarin lallai za a hukunta duk wanda aka samu da laifi, alkawarin da `yan kasa suke zaman jiran yadda za a karke.
Bayyana jadawalin zaben 2015, din ke da wuya, sai `yan siyasa, musamman na jam`iyyun adawa, suka fara kururuwar cewa jadawalin bai dace ba, kuma ba zai tabbatar da adalci ba, bisa ga irin yadda za a fara gudanadar da zabubbukan shugaban kasa da na `yan Majalisun Dokoki na kasa, makonni biyu, kuma a yi na gwamnoni da `yan Majalisun Dokoki na jihohi. Masu irin wannan ra`ayi na da`awar cewa gabatar da zabubbukan akan wannan tsari zai sanya gwamnonin jihohi su samu musgunawa da kuntatawa daga shugaban kasa da makarrabansa, musamman a jihohin da ya ga ba su zabe shi ba, musamman in ya yi nasara.
Masu irin wannan ra`ayi ba abin da suke bukata a wannan karon sai ganin Hukumar Zaben ta gudanar da dukkan zabubbukan a zaman falle daya kuma rana daya, kamar yadda aka dade a kasar nan ana begen ganin tabbatuwarsa, tun jamhuriya ta daya, tsarin da suka ce shi kadai zai tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zabe; kuma mai cike da gaskiya da adalci, duk abin ya gaza haka, to, kuwa zabubbukan na shekarar 2015, ba za su canja zane ba, in ji su.  
A ganina, kowane irin shiri Hukumar zabe za ta yi, don samun nasarar zaben, ba za ta kai ga nasara ba, sai kowa ya kama, kamawa kuma ta gaskiya da adalci. Abin da nike nufi a nan shi ne, nasarar zabe ta kowa da kowace, kama daga masu kada kuri`a zuwa `yan siyasa manya da kanana zuwa jami`an tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki cikin harkokin zabubbukan, sai kowa ya kama, cikin kamanta gaskiya da adalci, sannan ita kuma Hukumar zaben ta tabbatar da cewa wanda ya yi nasara, koda ana ha-maza ha-mata, to, lallai ta ba shi, sannan kuma duk wanda ya aikata kowace irin ba daidai ba, to a tabbatar da hukunta shi. Amma ba kowa ya yi abin da yake so ba, sannan kuma a rika mafarkin samun sahihin zabe, kamar yadda ake samu a kasashe irinsu Ghana da Afirka ta Kudu, to ya daina. Allah Ka nuna mana wancan lokaci, Ka kuma ba mu ikon zaben shugabanni nagari da za su kyautata mana.