✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar PCN ta rufe shagunan sayar da magunguna 343 a Kebbi

Majalisar Kula da Harhada Magungunna ta Kasa (PCN) ta sanar da rufe shagunan sayar da magungunna 343 a  kananan hukumomi 21 na Jihar Kebbi. Matakin…

Majalisar Kula da Harhada Magungunna ta Kasa (PCN) ta sanar da rufe shagunan sayar da magungunna 343 a  kananan hukumomi 21 na Jihar Kebbi.

Matakin ya biyo bayan rashin bin dokar sayar da magani na majalisar da kuma laifin rashin mallakar lasisin izinin sayar da magani da kuma kafa shagon sayar da magani a jihar ba bisa ka’ida ba da kuma sauran wasu laifuffuka, kamar yadda majalisar ta bayyana.

Daraktar Sashen Kula da Magunguna, Anthonia O. Aruya ne ta bayyana haka yayin taron manema a Birnin Kebbi. Ta ce yayin ayarin jami’an majalisar kula da harhada magungunna ta kasa suka zaga kananan hukumomin jihar ta Kebbi sun lura cewa da yawan masu sayar da magungunna a jihar suna sayar da su ne ba tare da bin ka’idoji ba, wanda dokar sayar da magani ta majalisar ba ta amince da haka ba.

Kananan hukumomin da matakin ya shafa sun hada da Birnin Kebbi da Gwandu da Bunza da Jega da Aliero da Maiyama da KoKo-Besse. Sauran su ne Argungu da Arewa da Yawuri da Shanga da Bagudo da kuma Kalgo.