Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa ta rarraba fiye da tan dubu 7 da na’ukan kayan abinci ga ’yan gudun hijirar da Boko Haram suka tarwatsa a Borno a cikin wata biyu.
Babban Ko’ddinatan Hukumar NEMA a banagaren agajin abinci a Arewa maso Gabas, Mista E. Umesi ya ce hukumar ta aiwatar da wannan aikin rabon ne ga ’yan gudun hijirar da ke Maiduguri da wasu karin wurare a yankin.
Gabanin haka kuma hukumar ta aiwatar da irin wannan aikin jinkai a lokuta da dama, inda ta ba da cikakken kulawa ga garuruwan Mafa da Dikwa da Gwazo da Bama da Benishek da kuma Jekuna da sauransu.
A yanzu haka hukumar ta yada zango a kananan hukumomin Biu da Hawul, inda ta raba tallafin kayan abinci a Biu da Kimba da Kwaja da Kwajafa da kuma Shafa. A takaice NEMA ta raba fiye da tirelolin abinci 200, sannan ayyukan rabon sun shafi fiye da garuruwa 10 da kauyukan da ke yankin. Kawo yanzu fiye da tan dubu 15 na abinci ne aka aike zuwa Borno, yayin da NEMA ta yi rajistar fiye da ’yan gudun hijira miliyan 1 da duba 800 a jihar.