✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NCC da masu ruwa- da-tsaki za su tallafa wa taron kirkira na Najeriya

Babban Ko’odineta na kasa na babban taron kirkira na Najeriya na shekarar 2019 da (NIS), Mista Tony Ajah, ya ce taron yana ci gaba da…

Babban Ko’odineta na kasa na babban taron kirkira na Najeriya na shekarar 2019 da (NIS), Mista Tony Ajah, ya ce taron yana ci gaba da samun goyon baya  da amincewa kafin ranar 20 da 21 ga Agusta da za a gudanar da shi a birnin Ikko da ke Jihar Legas.

Ajah ya bayyana haka ne a wata sanarwa inda ya ce hadin gwiwar ta zo ne daga Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), hukumar da ke sanya ido ga kamfanonin tarho na kasar nan wacce ke kan gaba wajen bunkasa kirkira da bincike da kuma bunkasawa.

Ya ce Hukumar NCC ta bayyana cewa goyon bayan taron kirkira na NIS yana daga cikin kokarinta na bunkasa kirkirar kimiyya da fasahar sadarwa da sanya jari da gudanar da hadin gwiwa don bunkasa tattalin arziki.

“Taron NIS wata dama ce ta musamman da za ta tattaro masu ruwa-da-tsaki a bangaren kimiyya da fasahar Najeriya don tattaunawa da samar da mafita da tsare-tsaren da za su zurfafa gudunmawar bangaren ga wasu masana’antu. Taron na hadin gwiwa wani taro ne na musamman da ake yi shekara-shekara wanda ke mayar da hankali kan bukatar da kasa take da ita ta hada-hadar kasuwanci da masana’antu da ’yan kasuwa su zama masu kirkira tare da yin amfani da kirkirar su bunkasa ci gaba mai dorewa. Manyan kirkira na fitowa ne daga bangaren kirkira da ya hada da gwamnati da ma’aikatun gwamnati da hada-hadar kasuwanci da kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu da bangaren ilimi da bincike da cibiyoyin bunkasa ci gaba da masu kamfanoni da masu kirkira da wadanda suka fara harkar kirkira. Kowane yana da rawar da yake takawa da aiki tare wajen cimma burin kirkira da bunkasa kimiyya a Najeriya. Wannan shi ne  abin da taron NIS ke son cimmawa.

Na wannan shekarar kamfanonin kasashen waje da na cikin gida da hukumomin gwamnati da ’yan kasuwa za su yi taro don ilimantarwa da fadakarwa da kuma karfafa ’yan Najeriya’’. Inji Ajah

Ya bayyana cewa taron wanda kofarsa a bude take ga wadanda suke son shiga zai taimaka wa Najeriya ta rungumi kirkira da sanya ta bin tafarkin bunkasa kimiyya da fasaha.

Ya ce taron zai gudana ta hanyar yin amfani da fasahar zamani da bincike da bunkasawa da hada-hadar cinikayya, sanya jari a matsayin muhimman mabudai ga harkokin kirkira.

Ajah ya bayyana cewa  taron zai wayar da kan jama’a kan bukatar da ake da ita na kirkira a Najeriya da kalubale da Najeriya za ta yi amfani da shi kan kirkira ta yadda za ta yi gogayya a tattalin arzikin duniya.

Ya bayyana cewa wadanda za su yi jawabi a taron sun hada da Farfesa Umar Garba Dambatta, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa da Obinnia Abajue, Babban Jami’i na Kamfanin Hygeia da Bruno Woeran, Manajan Harkokin Kungiyar Turai, da Cibiyar Bunkasa Kimiyya ta Merinoba Finlanda da Tosin Faniro-Dada, Shugaban Kamfanin Startups da ke Jihar Legas da Asusun Samar da Ayyukan Yi na Jihar Legas da Farfesa Nii Kuaynor na Kamfanin Africa Internate Pioneer.

Sauran sun hada da, Shugaban Kamfanin Ghana Dot Com, Adesola Alli, Shugaban Kamfanin Renewable Energy, Dabaru da Kirkira na Bankin Sterling Bank Plc, Farfesa Wellington Oyibo, Daraktan Bincike na ofishin Kirkira na Jami’ar Legas da sauransu.

Haka ma akwai Asusun Samar da Ayyukan yi na Jihar Legas da Jami’ar Jihar Legas da Jami’ar Landmark da Jami’ar Mountain Top da Jami’ar Igbinedion da Jami’ar Fatakwal duk sun tabbatar da za su halarci taron haka ma Jihohin Bauchi da Kano da Edo da Ondo duk sun bayar da tabbacin za su halarci taron da sauran kamfanoni da ma’aikatu daban-daban.

Ya bayyana cewa taron NIS ya shiga shekara ta hudu kuma wani tsari ne  wanda kamfanin tallace-tallace na Emerging Media and Adbertisement Serbices da ke Birnin New York da hadin gwiwar Kamfanin Emerging Media na Najeriya da goyon bayan Kamfanin TechEconomy.ng suka shirya.

Ya bayyana cewa jigon taron shi ne “Gaggauta Bunkasar Tattalin Arzikin Najeriya ta hanyar Kirkira”.

Wanda zai jagoranci taron shi ne Shugaban Kamfanin Emergin Media, Kenneth Omeruo ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su kwaikwayi Hukumar Sadarwa ta NCC wajen tallafa wa kirkira a kasa baki daya.

Ya bayyana Najeriya ita ce ta 114 daga cikin kasashe 129 da suka cigaba a harkar kirkira. Ya ce kuma hakan ba a bin amincewa ba ne.

“Mun karfafa jagori kan kirkira na duniya daga bangaren jami’o’i da gwamnati da masana’antu su hada gwiwa da mu don hada ’yan kasuwar Najeriya da masu kirkira a bangaren kirkira na duniya,” inji shi.