Hukumar Hisbah tare da hadin gwiwar masu gidajen biki a Jihar Kano za su yi yaki da rashin da’a ta hanyar sanya jami’ansu su rika sa ido a wuraren biki da dakunan taro da na shakatawa da ke fadin Jihar domin haramta shan Shisha.
An cimma wannan yarjejeniyar tsakanin shugabanin masu wuraren taro da gidajen siyar da abinci da na wuraren shakatawa a wani zama da su ka yi da Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina.
- Za mu kawar da ayyukan ta’addanci a Katsina — Babban Sufeton ‘Yan Sanda
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara
Cikin takardar kulla yarjejeniyar mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar Hisba, Lawan Ibrahim Fagge, ta ce Jami’an Hisbah za su kuma rika sanya idanu kan gidajen kallon kwallon kafa da ke fadin Jihar don dakile shaye-shaye da dangoginsu.
Kazalika, sanarwar ta ce Hukumar za ta yi kokarin kare yara masu kananan shekarau daga fada wa shaye-shayen Shisha a cibiyoyin.