✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Birnin Abuja ta yi hadin gwiwa da NCC dangane da harkokin sadarwa

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) da Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC) sun yi hadin gwiwa domin magance matsalolin da ake samu…

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) da Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC) sun yi hadin gwiwa domin magance matsalolin da ake samu dangane da al’amuran sadarwa a birni da kewaye.

Mataimakin Shugaban hukumar, Farfesa Umar danbatta ne ya bayyana haka, a lokacin da ya kai wa Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello ziyara a ofishinsa, Abuja.

“La’akari da matsayin Abuja a yau, ya dace a ce tana da ingantattun hanyoyin sadarwa, sai dai ba haka abin yake ba har zuwa yau. Wannan ya tabbatar mana da hakikanin yanayi, cewa Abuja tana fuskantar wasu kalubale da ke kawo cikas wajen tabbatar da juyin-juya-hali a harkar sadarwa nan gaba. Babban Birnin Tarayya na da matsaloli mafiya wuyar sha’ani, wajen samun ingantattun hanyoyin sadarwa, idan aka kwatanta shi da sauran birane a fadin kasar nan, saboda wasu dalilai da nan gaba za mu kara haske a kansu,” kamar yadda shugaban na NCC ya shaida wa Ministan Babban Birnin Tarayya.

Ya zayyana wasu daga cikin matsalolin da suka hada da girke tashoshin sadarwa a Abuja, kudin haraji da Babban Birnin Abuja ke amsa daga kamfanonin sadarwa tun a 2006, dokokin da suka shafi harkokin sadarwa kan al’amuran da suka faru a Abuja, matsalolin gine-ginen hanyoyi a Abuja, jinkirin da ake samu wajen bayar da izinin kafa tashoshin sadarwa ko canja masu matsuguni da kuma dabbaka kudurorin da Majalisar Zartarwa ta kasa ta gindaya dangane da ninkin kudin haraji ko tara da ake amsa game da kayayyakin kamfanonin sadarwa.

Game da batun girke tashar sadarwa, Shugaban NCC ya ce kamfanonin a shirye suke su girke tashoshin nasu amma “har yanzu ba mu samu bayanin ka’idojin yin haka ba daga hukumar Babban Birnin Tarayya.”

Ya kara da cewa: “Muna rokon Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta amince da ka’idojin hukumar NCC dangane da kafa tashar kamfanin sadarwa. Haka kuma, wuraren da aka ware domin kafa tashoshin sadarwa sun yi kadan kuma ba su dace da tsarin da kamfanonin ke bukata ba. Ya dace a ce ana musharaka da kamfanonin sadarwa, kafin a ware masu wuraren da ake tanadar masu, domin kafa tashoshinsu, domin su dace da samun netwok da kuma yanayin da ya dace da masu kafa tashar rediyo. Haka kuma, idan har an lura da cewa wuraren ba za su iya daukar tashar sadarwa ba, to hukumar FCT ta amince wa kamfanonin su ci gajiyar kashin kansu.

Dangane da batun dokokin kudi da suka shafi sadarwa na 2006 kuwa, ya ce a sakamakon wani taro da hukumar NCC ta yi da hukumar FCT a waccan shekara, an amince cewa hukumar ta FCT za ta zauna ta dauki mataki a kan kudi masu yawa da ake amsa kafin ba da takardar amincewa a yi gini a babban birnin.

“Ba a kai ga yin haka ba kuma kamfanonin sadarwa na ci gaba da amsar kudaden da aka kayyade a 2006. Saboda haka, ina rokon amincewarka da a kafa kwamiti, wanda zai hada da jami’an FCT da na NCC, domin magance matsalar nan da ta danganci amsar kudi masu yawa, kamar yadda za a rika amsar kudi daidai da yadda ake amsa a hannun sauran kamfanonin da ba na sadarwa ba,” inji Farfesa danbatta.

Dangane da dokokin da suke waigen baya, dangane da abin da ya shafi kayayyakin kamfanonin sadarwa kuwa, shugaban NCC ya ce duk dokar FCT irin wannan da ta shafi kayayyakin kamfanonin sadarwa, bai kamata ta rika waiwayen baya ba.

“Mun ankara da cewa a lokacin da kafa irin wadannan dokoki, ba a yi la’akari da kamfanonin sadarwa ba, domin a lokacin babu su, wanda dalili ke nan yanzu hukuma ke daukarsu kamar sauran kamfanoni, suna kawo masu dokoki wadanda ba su dace da su ba. Saboda haka muna rokon cewa a rika amincewa da kamfanonin sadarwa wadanda suka riga suka kafu a Abuja, sai dai kawai wadanda ake ganin kamar suna kawo barazana ga makwabtansu,” inji shi.

Haka kuma ya shaida wa ministan cewa kamfanonin sadarwa sun yi wa sashin gine-gine na FCDA korafin cewa a yayin gine-ginen hanyoyi a Abuja, kamfanonin gini suna katse masu wayoyinsu na sadarwa. “Irin wadannan matsalolin na yankewar wayoyin sadarwa yana haddasa rashin sabis ga masu amfani da wayoyi, wanda haka ke ta’azzara matsalolin sadarwa a Abuja da kewaye. Duk da iri kokarin da Sashin Kula Da Gine-Gine na FCDA ke yi domin magance wannan matsalar, har yanzu ana ci gaba da samun katse-katsen wayoyin. Ya kamata a fahimtar da kamfanonin gine-gine da su yi hattara, su rika kiyayewa domin ragewa ko daina katse wayoyin sadarwa a yayin gudanar da aikace-aikacensu,” inji shugaban na NCC.

Game da jinkirin da ake samu na kafa tashoshin sadarwa kuwa, ya ce akwai takardun bukatun kafa tashoshin a Abuja da kamfanoni suka aika tun 2014, amma har yanzu suna kan jira. Haka kuma ya ja hankalin minista game da daftarin kudurorin da Majalisar Zartarwa ta kasa ta gindaya dangane da ninkin kudin haraji ko tara da ake amsa game da kayayyakin kamfanonin sadarwa. Ya ba da shawarar cewa ya kamata a rarraba wa jami’an ma’aikatar domin dabbakawa.

Tun da farko, shugaban na NCC ya ce kudaden da Sashin Kimiyyar Sadarwa (ICT) ke samarwa duk bayan wata uku ga asusun kasa ya karu zuwa Naira tiriliyan 1.6 daga tiriliyan 1.4. Ya kara da cewa Sashin Kimiyyar Sadarwa yana bayar da gudunmuwar kusan kashi 10 cikin dari na Kudaden Shigar kasa a duk shekara.

Ya ce masu amfani da intanet a kasar nan sun karu, inda a yanzu suka kai mutum miliyan 92 a watan Yunin da ya gabata. Ya ce babban tsarin nan na rarraba intanet (broadband), ana sa ran zai cin ma kashi 30 cikin dari zuwa badi, wanda haka zai sanya masu amfani da intanet su karu a kasar nan. “Harkokin sadarwa sun haifar da zuba jarin masa da Dala biliyan 68 daga ’yan kasuwa masu zaman kansu tun daga 2001,” inji shi.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Musa Bello, a nasa bangaren ya dauki alkawarin cewa hukumar FCT za ta hada gwiwa da NCC domin magance wadannan matsaloli da aka bijiro da su. “Wani bangare na aikinmu shi ne mu saukaka hanyoyin gudanar da sana’o’i da kara zuba jari a birnin da ma kasa baki daya. Za mu tallafa wajen ganin cewa an samu karuwar tsarin inganta iuntanet a sassan kasar nan, inji Malam Bello.

Ya yi alkawarin cewa zai kafa kwamiti, wanda zai bi kadin dukkan korafe-korafen da NCC ta bijiro da su. Ya shaida wa shugaban na NCC da ya kwantar da hankalinsa kuma ya ci gaba da tuntubarsa kai tsaye, da zarar an magance matsalar da yake kuka a kanta.