✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Alhazan Kaduna ta roki maniyyata su cikan kudin kujera

Sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, Salihu Abubakar, ya roki limamai su taimaka wajen wayar da kan maniyyata su kokarta cika kudin kujera Hajji…

Sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, Salihu Abubakar, ya roki limamai su taimaka wajen wayar da kan maniyyata su kokarta cika kudin kujera Hajji bana kafin ranar 31 ga watan nan Disamba da muke ciki.

Malam Salihu  ya ce akwai bukatar a tuna wa maniyyata cewa har yanzu ana karbar kudin kujera, saboda nan da ’yan kwanaki za a rufe karbar kudin kujera da aka nemi duk maniyyaci ya biya Naira miliyan 4 da rabi.

Ya Kuma shawarci maniyyata da su tabbatar da sun karbi takardun bankin a ofishoshin Hukumar Dake a kananan hukumomi 23 a jihar domin zuwa su biya kudin kujerarsu.

“Muna tabbatar wa maniyyata cewa za mu tabbatar da an rike masu amanar dukiyarsu kuma har yanzu ana ci gaba da karbar kudin kujerar har zuwa ranar 31 ga watan nan na Disamba” in ji shi.

Ya ce ana bukatar Hukumar Alhazan ta mika kudaden wadanda suka biya kujerarsu ga Hukumar Aikih Hajji ta Kasa (NAHCON) a ranar 5 ga watan Janairu 2024, kamar yadda dokar Hukumar ta tanadar, shi yasa ake kira ga sauran maniyyata da su kokarta su kammala cikan kudinsu.