✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano

Hukumar ta ce tana ƙoƙarin gano sauran da suke da hannu wajen aikata badaƙalar.

Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki.

Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin.

An gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban.

Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed.

Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa.

Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya.

A cewar hukumar Mohammed, yana bayar da haɗin kai wajen binciken, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin bankaɗo cikakkun bayanai game da badaƙalar.

Hukumar ta jaddada ƙudirinta na yaƙi da cin hanci da tabbatar da gaskiya a tafiyar da shugabanci.