✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Zikirin Juma’a Na Shekara-Shekara A Fadar Sarkin Kano

Bayan zikiri an gudanar da addu'o'in neman samun zaman lafiya a fadin Nigeria

A ranar Juma’a ne aka gudanar da Zikirin Shekara tare da adduo’i da aka saba yi a Fadar Sarkin Kano.

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ne ya jagoranci zikirin na bana, wanda baki daga ciki da kuma wajen jihar suka halarta.

Ga kayatattun hotunan yadda zikitin  ya kasance.

Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Mataimakin Gwamnan Kano Yusuf Gawuna a wajen Zikirin (Hoto: Saudat)
Mai Martaba Sarkin Kano tare da wasu manyan baki a wurin zikirin da ya gudana a fadarsa. (Hoto: Saudat).
Wani sashe na jama’ar da suka taron suna tsaka da yin zikiri a Fadar Sarkin Kano. (Hoto: Saudat).
Wasu karin jama’ar da suka halarci taron zikirin. (Hoton: Saudat).
Karin wasu mahalarta taron da ya gudana a Fadar Sarkin Kano. (Hoton: Saudat).
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Mataimakin gwamna jihar, Yusuf Gawuna da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, a lokacin taron zikirin. (Hoton: Saudat).

Wasu daga cikin matan da suka halarci zikirin daga bangare guda. (Hoto: Saudat)

Mata ma ba a bar su a baya ba (Hoto: Saudat).
Wasu baki daga ciki da kuma wajen Kano da suka halarci zikirin (Hoto: Saudat).
Komawar Mai Martaba Sarkin Kano gida bayan an kammala zikirin da kuma adduo’i a ranar Juma’a. (Hoton: Saudat).