✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda zamanantar da sana’ar zayyana ya kai ga kafa mata makaranta a Kano

Yanzu dai an zamanantar da wannan sana'ar, ta tashi daga ta gargajiya

A da, an fi sanin zayyana watau adon zane-zane da ake yi wa allon da ake ba masu saukar karatun Al-Kurani a makarantun tsangaya da Islamiyyu, amma yanzu wannan sana’ar ta bunkasa a jihar Kano.

Bunkasar sana’ar ta samu ne ta hanyar zamanantar da yanayi da tsarinta da kuma yin ta a wurare daban-daban kamar fatoci, da takarda, da bango da kuma sauran wurare domin ya kayatar.

Hakan ya kai ga kafa wata makarantar da ake koyar da wannan fasaha ga matasa maza da mata masu sha’war koyon zane ta fasahar zamani, mai suna Gabari Institute of Islamic Calligraphy And Geometric Design a Kano.

Ga wasu daga cikin kayatattun hotunan wannan ci gaban fasahar zayyana a zamanance.

Zayyanar Allo na gargajiya wanda shugaban makarantar ya ke yi na gado (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Allon da aka yiwa zayyana wanda ake rabawa dalibai a matsayin shaidar sauke AlKurani mai girma (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Malama Mustapha na amfani da na’urorin zamani domin ya mayar da wannnan fasahar zayyana jikin wasu abubuwa na ado (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Amfani da basirar zayyana ta gado da kuma fasahar zamani wajen yin zane wannan gudanar da aikin a zamance (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Wasu zanuka na zamani da Mustapha Gabari ya yi daga basirarsa ta zayyana. (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)

 

Yayin aikin zayyana ta zamani a jikin bango (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Amfani da basirar zayyana a zamanance don samar da hotunan ado a takarda (Hoto: Gabari Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Yadda zanen ya ke bayan an gama shi da zayynar zamani (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Amfani da wannan fasaha wajen kikkirar zanen da ya dace a bango (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Yadda aka yi zanen a wasu wuraren a makarantar daga dalibai (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Wani nau’in zanen da ake yi da siminti, sannnan a bi shi da launuka (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Nau’in zanen a jikin fata na ado, yayin da Mustaph Gabarai ke aiki a kai. (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Daya daga cikin zanukan samfurin zayyanar zamani a jikin aikin fata (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Samfurin aikin zayyanar a jikin kujerar zaman da aka yi da fata.(Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Malam Mustapha na zayyana da sunayen Allah da aka kawata domin ado. (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Irin wannan zayyana da aka yi na sunayyen Allah a matsayin rataye na ado. (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Shugaban makarantar na nuna wa baki wasu daga cikin dalibai da ke samun horo kan zayyana ta zamani (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Daya daga cikin dalibai mata da ke koyon zayyanar a bakin aikin yayin da wasu baki su ka ki ziyara makarantar (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Wasu daga cikin zayyanar ta zamani da daliban suka yi a domin sa wa a daki da sauran wurare a gida. (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs)
Shugaban makarantar Mustapha Gabari da Farfesa Abdallah Uba Adamu a kofar rumfar makarantar bikin bajekoli da ta halarta (Hoto: Gabari Institute of Islamic Calligraphy & Geometric Designs).