✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda Shettima ya kaddamar da bude Masallacin Majalisar Wakilai

Shettima ya ja hankalin shugabanni wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da Masallacin Juma’a da al’ummar Musulmi suka gina a majalisar dokoki.

Aminiya ta ruwaito cewa, Shettima ne ya wakilci Shugaban Kasa Bola Tinubu a wajen taron bude Masallacin.

Da yake jawabi, mataimakin shugaban kasar, ya ce, ya je bude Masallacin ne don taya al’ummar Musulmi murna a Majalisar Dokokin.

Ya kuma yi kira ga shugabanni da su kasance masu tawali’u yayin da suke sauke nauyin da aka dora musu a lokacin da suke rike da madafun iko da kuma neman lahirarsu ta hanyar samar da irin wadannan ayyuka da kuma sadaka.

Ga hotunan a kasa: