✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano

Haruna Zago ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano.

Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya.

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi.

Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin.

Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana: