✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta dawo da kwamandan da ake zargi da cinye kayan tallafi

Hisbah ta Jihar Kano ta dawo da kwamandanta da ta dakatar bisa zargin karkatar da kayan tallafi.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta dawo da kwamandanta da ta dakatar bisa zargin karkatar da kayan tallafi.

Hisbah ta ce ta dawo da Suyudi Muhammad Hassan, wanda shi ne kwamandanta na Karamar Hukumar Dala bakin aikinsa ne bayan binciken da ta gudanar kan zargin bai same shi da laifi ba.

“An umarce ni da in sanar cewa Babban Kwamadan Hukumar ya amince a dawo da Suyudi Muhammad Hassan bakin aiki a matsayin Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Dala,” inji sanarwar.

Sakon da dauke ne da sa hannun mataimakin sakatare Hukumar, Muhammad Babangida D/Iya.

A baya an dakatar da Kwamandan na Hisbah ne bisa zargin sa da karkatar da kayan tallafin COVID-19.

Sakamakon zargin, Hukumar ta kafa kwamitin bincike domin binciko gaskiyar lamarin, wanda a halin yanzu ya wanke shi daga zargin da cewa an yi ne domin goga masa kashin kaji.