✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hazard ya fara tunanin komawa Madrid

Dan kwallon kulob din Chelsea na Ingila Eden Hazard a ranar Talatar da ta wuce ya sake nanata niyyarsa ta barin kulob din Chelsea a…

Dan kwallon kulob din Chelsea na Ingila Eden Hazard a ranar Talatar da ta wuce ya sake nanata niyyarsa ta barin kulob din Chelsea a karshen kakar wasa ta bana.

Hazard, dan asalin Beljiyam, tun bayan da aka kammala gasar cin Kofin Duniya a Rasha ya bayyana yiwuwar barin Chelsea a karshen kakar wasa ta bana.

Yunkurin da kulob din ya yi na sabunta masa kwantaragi ya ci tura, inda dan kwallon da kansa ya ce komai zai iya faruwa kuma hankalinsa ya fi karkata ne zuwa kulob din Real Madrid na Sifen.

Rahotanni sun ce Hazard ya ki amincewa da sabon kwantaragin da Chelsea ta yi masa tayi kuma hakan ya nuna lallai akwai yiwuwar ya bar kulob din a karshen kakar wasa ta bana zuwa kulob din Real Madrid na Sifen.