Mai rikon mukamin kamfanin sufurin jiragen sama na Nigeria Air, Kyaftin Dapo Olumide, ya ce jirgin da ya zo Najeriya da sunan kamfanin hayarsa suka dauko daga Habasha.
Shugaban ya amsa cewa sun nuna alamar kamfanin ne kawai ba wai kaddamar da fara aikinsa ba, bayan sun dauko shi daga kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airline, mallakin kasar Habasha.
- Saudiyya ta ba Najeriya kyautar tan 50 na dabino
- Rushe gine-ginen da gwamnatin Kano take yi aikin jahilci ne – APC
Jirgin dai ya iso Najeriya ne ranar Juma’a, ana saura kwana uku Muhammadu Buhari ya sauka daga Shugabancin Najeriya, dauke da tambarin Nigeria Air.
An dai yi ta nuna shakku a kan ingancin mallakar jirgin, inda daga bisani bincike ya nuna ko ana kwana hudu kafin zuwansa Najeriya sai da kamfanin na Habasha ya yi amfani da jirgin daga birnin Addis Ababa na Habasha zuwa Tel Aviv na Isra’ila.
Amma bayan ya bayyana a gaban Kwamitin Sufurin Jiragen Sama na Majalisar Wakilai a ranar Talata, Kyaftin Dapo ya ce har yanzu kamfanin bai kai ga samun cikakken izinin fara zirga-zirga ba, har yanzu akwai ragowar matakai.
Ya ce an yi amfani da jirgi ne ya zuwa lokacin da za a kammala matakan da za su nayar da dama a yi amfani da shi.
“Kawai mun dauko hayarsa ne domin mu nuna wa ’yan Najeriya da sauran wadanda suka zuba jarinsu a harkar yadda jirgin zai kasance, amma ba wai aiki ya fara ba. Kowa kuma zai iya daukar hayar jirgi,” in ji Shugaban kamfanin.
Tun da farko sai da Shugaban Kwamitin Majalisar, Sanata Biodun Olujimi, ya nuna takaicinsa kan yadda ya ce tsohon Ministan Sufuri, Hadi Sirika, ya ki tafiya da su don sanin abubuwan da ke wakana a shirye-shiryen dawo da kamfanin jiragen.