✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawa da Fulanin Kurmi sun karfafa batun hadin kai da zaman lafiya

Sarakunan Hausawa da Fulanin jihohin Kudu maso Yamma shida sun yi babban taro a Ibadan, inda suka tattauna  muhimman abubuwan da suka hada da hadin…

Sarakunan Hausawa da Fulanin jihohin Kudu maso Yamma shida sun yi babban taro a Ibadan, inda suka tattauna  muhimman abubuwan da suka hada da hadin kai tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani da kuma zamantakewarsu  da jama’ar garuruwan da suke zaune don samun zaman lafiya a sashen da kasa baki daya.

An gudanar da taron ne a karkashin shugabancin Sardaunan Yamma, kuma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin a fadarsa da ke Sasa a Ibadan. Sarakunan Hausawa da Fulani fiye da 50 ne suka  halarci taron.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, Ardon Zuru Alhaji Muhammadu Kiruwa da Shugaban Kungiyar a Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello ma sun halarci taron na Ibadan.

Bayan Sarakunan sun tofa albarkacin bakinsu a kan wadannan batutuwa tare da nuna goyon bayansu da jagorancin da Sarkin Sasa ke yi sai taron ya yanke shawarar kafa kwamiti mai wakilai 21 na sarakunan Hausawa da Fulani. Kowace jiha za ta aike da wakilai uku da za su yi zaman farko nan da mako biyu domin kafa kananan kwamitoci na tuntunbar gwamnatocin jihohi 6 na sashen da jami’an tsaro da manyan sarakunan Yarbawa domin sanar da su manufar sarakunan Hausawa da Fulanin don neman shawararsu wajen lalubo hanyar hada kai da zama lafiya a tsakanin jama’a.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani kan taron, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya ce, “Taron ya umarci kowane Sarkin Hausawa da Fulani ya koma garinsa ya zauna da hakimansa da shugabannin kungiyoyi da malaman addinin Musulunci domin tattaunawa a kan wannan al’amari da ya shafi tsaron kasa baki daya. Kuma taron namu ya amince da daukar matakin hana matasanmu shaye-shayen miyagun kwayoyi da hana su shiga bangar siyasa inda wadansu ’yan siyasa suke amfani da su wajen tayar da zaune-tsaye.”

“Ina kira ga jama’armu baki daya da ke zaune a wannan sashe su zauna lafiya ban da tsokanar fada. Kada ku bari a yi amfani da ku wajen hargitsa kasa, musamman a wannan lokaci na shirin zaben kasa. Idan wata matsala ta taso a tsakaninku da mutanen gari, ku hanzarta sanar da shugabanninku ko ofishin ’yan sanda; ku girmama doka da oda. Kada ku yanke wa kanku hukunci,” inji shi.

A kwanakin baya Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya aza harsashin gina fadar Sarkin Ibo a Kano. A lokacin Sarki Sanusi ya amince da sanya Sarkin Ibo da Sarkin Yarbawa a cikin sunayen hakimai da masarautar Kano take biyan su albashi a kowane wata.

Binciken Aminiya ya gano cewa duk da dadewar sarakunan Hausawa a Kudu, ba a taba samun wata masarauta ko gwamnatin sashen da ta taba biyan albashi gare su ba, duk da amfanin da ake yi da su a lokuta daban-daban wajen isar da sakon mahukunta ga jama’arsu.