Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan mata bakwai sun rasa rayukansu bayan da kwale-kwalen da suke tafiya a ciki ya kife ranar Alhamis da dare a Jihar Jigawa.
BBC ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne lokacin da suke kokarin tsallaka wani kogi a kan hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi a garin Gasanya.
- Na yi alkawari zan yi nazari kan sakin Nnamdi Kanu — Buhari
- Za a bai wa kowace jiha tallafin N18bn — Buhari
Bayanai sun ce jirgin na dauke da mutum 12 ne lokacin da ya kife a cikin kogin wanda ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa, inda bakwai suka rasu, biyar suka tsallake rijiya da baya.
Mutanen dai na kan hanyarsu ne ta komawa garinsu na Gafasa da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa daga Gasanya na Karamar Hukumar Auyo.
Malam Mikail Jibril daya ne daga cikin iyayen waanda suka rasu, kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa shekarun ‘yan matan bai wuce 11 ba zuwa 12.
Mai garin na Gafasa Alhaji Adamu Abdullahi ya ce tuni aka yi jana’izarsu.
A watan Mayun wannan shekarar, mutum fiye da 100 sun rasa rayukansu sakamakon irin wannan hatsarin na jirgin ruwa da ya afku kusa da garin Warah na Jihar Kebbi duk a yankin na arewa maso yammacin Najeriya.