✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin Jirgi: Dana Air ya sallami ma’aikata

Sallamar ta wucin-gadi ce har zuwa lokacin da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama NCAA za ta kammala bincike.

Kamfanin Jiragen Sama na Dana Air ya sallami wasu daga cikin ma’aikatansa bayan dakatar da harkokinsa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya NCAA ta yi.

A halin yanzu dai hukumar ta NCAA na ci gaba da gudanar da bincike kan kamfanin jiragen bayan hatsarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin jiragensa a makonnin baya bayan nan.

Sai dai Aminiya ta ruwaito cewa sallamar ma’aikatan da kamfanin jiragen ya yi ta wucin-gadi ce gabanin hukumar ta NCAA ta kammala  binciken da take gudanarwa.

Shugaban sashen sadarwa na Kamfanin Dana Air, Kingsley Ezenwa, ya tabbatar da sallamar ma’aikatan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sai dai ya ce kamfanin ya ɗauki matakin ne a yunƙurin bai wa hukumar ta NCAA haɗin kai dangane da binciken da take gudanarwa a kansa.

Sanarwar ta ƙara jaddada manufarta ta bai wa mahukunta haɗin kai, dalili ke nan da ta dakatar da wasu ma’aikatan har zuwa lokacin da za a kammala binciken.

Mista Ezenwa ya miƙa godiyar kamfanin ga ɗaukacin ma’aikatan musamman kan jajircewa da juriyar da suke nunawa a wannan lokaci na rashin tabbas.

Ya ce kamfanin yana sane da irin ƙuncin da ma’aikatansa ke fuskanta yana mai jaddada cewa suna duk mai yiwuwa don ganin sun saukaka musu lamarin cikin gaggawa.