✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsari ya ritsa da ayarin motocin Gwamnan Delta

Mutum biyu sun tsallake rijiya da baya a hatsarin motocin Gwamnan Delta a hanyarsa ta dawowa daga wani taro.

Mutum biyu sun tsallake rijiya da baya da munanan raunuka bayan ayarin motocin Gwamnan, Sheriff Oborevwori sun yi mummunan hatsari.

Majiyarmu ta ce diraben daya daga cikin motocin da wani hadiman gwamnan ne suka samu rauni a hatsarin, sakamakon fashewar tayar motarsu a yayin da suke tsaka da tafiya.

Aminiya ta gano cewa an kai mutanen da abin ya shafa suna  asibiti domin basu kulawa sakamakon hasarin a Asaba, fadar jihar.

Zuwa lokacin hada wannan labarin dai babu cikakken bayani game da asarar rai, amma majiyar  ta ce hatsarin ya auku ne a kusa da Kwalejin Ilimi na Tarayya (Technical) da ke Asaba.

“Muna cikin motar haya a hanyar dawowa Asaba ne muka ji kara kamar harbi, nan da nan aka samu cunkoson ababen kafin a kai su asibiti,” in ji majiyar.

A karshe mako ne Gwamna Sheriff Oborevwori ya kai ziyara garin Warri domin halartar taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP ranar Lahadi gabanin zaben kanana hukumomi da ke tafe.

A hanyarsa ta komawa Asaba ne ayarin motocin nasa ya samu hatsar a safiyar Litinin.