✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsari ya ci mutum 2, wasu 5 sun jikkata a hanyar Abuja-Kaduna

Wani ganau, ya ce hatsarin ya faru sakamakon gudun wuce kima da rashin kyawun titi.

Fasinjoji biyu sun rasu, wasu biyar sun jikkata a wani hatsarin mota da a hanyar Kaduna zuwa Abuja a yammacin ranar Lahadi.

Wani ganau, Malam Nasir Idris, wanda yake bayan motar, ya ce an yi taho-mu-gama ne tsakanin wata mota kirar Golf dauke da mutum bakwai da wata Marsandai wadda direbanta ne kadai a ciki lokacin da hatsarin ya auku.

“Hatsarin ya faru ne saboda gudun wuce gona da iri, amma rashin kyawun titin ya taimaka wajen faruwar hatsarin,” in ji shi.

A cewarsa, Golf din na kan hanyar zuwa Kaduna ne, yayin da daya motar ta nufi Abuja.

Ya ce an kai wadanda suka mutu A hatsarin wani asibiti a Kaduna da misalin karfe 5:30 na yamma.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), a Jihar Kaduna, bai amsa kiranmu ba na neman karin bayani kan abin da ya faru, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.