✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hasashen Hukumar NIMET kan karancin ruwan sama

A makon jiya ne Hukumar Kula da Yanayin ta Najeriya (NIMET) ta ce akwai yiwuwar a samu karancin ruwan sama a bana, inda ta shawarci…

A makon jiya ne Hukumar Kula da Yanayin ta Najeriya (NIMET) ta ce akwai yiwuwar a samu karancin ruwan sama a bana, inda ta shawarci manoma su yi shuka da wuri. Sai dai mutane da dama ba su dauki shawarar da muhimmanci ba.
Wasu ma cewa suka yi has ashen na NIMET a bara bai tabbata ba, domin ta ce zaa samu ruwan sama mai yawa a sassan kasar nan da zai jawo ambaliya amma ba a samu haka ba.
Idan ya zamo cewa saboda gargadin NIMET bai tabbata ba za a yi sakaci, wannan ba zai haifar da da mai ido ba, domin has ashen hukumomi irin su NIMET yana iya dogara ne da wasu abubuwa da dama. Muhimmin sakamakon da za a samu shi ne a fahimci cewa kasar nan ta dogara galibi kan ruwan sama yayin gudanar da ayyukan nomanta.
Yana da sauki a gano hadarin da ke cikin haka, saboda yana nufin cewa kokarin noma a kasar nan ba zai cimma nasarar kirki ba, idan aka samu karancin ruwa sama a bana. Kuma abin da zai biyo baya shi ne kasar nan za ta fuskanci bala’in karancin abinci. Kuma idan kamar yadda NIMET ta yi hasashe a matsayin gargadi cewa ruwan sama zai  yi karanci, yana iya yiwuwa ba zai sauka da wuri ba a wadace yadda manoman da suke son yin shuka za su iya yin haka da farko kamar yadda aka shawarce su.
Domin haka ya wajaba a dauki shawarar NIMET a matsayin abin lura a tsakanin masu ruwa da tsaki a bangaren aikin gona. Wajibi ne a dauki matakan da za a kwantar da hankali da dardar din da manoma za su shiga da ka iya kashe musu gwiwa ko ya rikitar da su kan yadda za su kauce wa yin asara. Kuma babu dalilin da zai sa a tsaya ana kai-kawo kan hakan zai faru ko ba zai faru ba.
Gargadin na NIMET wata tunatrwa ce kan hadarin da ke cikin dogaro da noman damina don ciyar da kasa da abinci, wanda ba ya da tabbas kuma hadari ne ga shirin samar da wadataccen abinci ga kasa. Duk da cewa Najeriya tana da dimbin madatsun ruwaani a sassan kasar nan, mafi yawansu ba su da wani amfani. Madatsar ruwa ta Tiga da ke Kano wadda ita ce mafi girma a Afirka ta Yamma da sauransu musamman a nan Arewa, ba a amfani da su yadda ya kamata, ko ma ba a amfani da su ko kadan domin noman rani da na lambu ko samar da wutar lantarki.
Madatsar Tiga dai ta tsaya cik sama da shekara 30. Wannan abin kunya ne ga kasar da take da dimbin matasa marasa aikin yi, kuma aikin gona yana baya sosai inda take dogara da shigo da abinci daga kasashen waje na biliyoyin Dala a kowace shekara.
Baya ga madatsun ruwa har wa yau kasar nan tana da kasar noma mai albarka, wadda idan muka yi amfani da ita yadda ya kamata za mu yi gagarumar inganta aikin gona. Miliyoyin kananan manoman kasar nan sun dogara ne da kayan aikin gona na gargajiya da kananan gonaki da aka dade ana noma su sakamakon haka albarkarsu kullum baya take yi. Hakika wannan bai dace ba, bisa gargadin na NEMIT da kuma shi kansa gudanar da aikin gona a kasar nan a dogon lokaci.
 Don haka wajibi ne Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin da a yankunansu ne madatsun ruwan suke su tsara tare da shirya wasu dabaru cikin hanzari kan yadda za su tattaro manoma don taimaka musu da sababbin dabarun noma da kayan aiki kan yadda za su iya gudanar da noma mai inganci da bai dogaro da ruwan sama.
Ta amfani da ilimi da dimbin kayayyakin noma na zamani da dabarun noma da ake da su, ba shawara ce mai kyau ba a ci gaba da dogara da ruwan sama wajen noman abinci a kasar nan. Noma a yanzu ba kawai harka ce ta neman abin sawa a bakin salati kadai ba, ya zama babban aikin da ke bayar da gudunmawa wajen samar da karin kudin shiga ga kasashe da dama. Kuma bai kamata Najeriya ta fita daban a wannan bangare ba, duk da dimbin albarkatun man da take da shi ba.