Wasu ’yan daba sun kai hari unguwar Kurnar Asabe da ke Karamar Hukumar Dala a Kano, inda suka raunata mutane da dama tare da yi musu fashi.
Limamin unguwar Malam Hamisu Maigemu ya ce, “’Yan daban sun fi 100 suka zo, kuma sun soki fiye da mutane 20 kafin a samu nasarar fatattakar su da taimakon jami’an tsaron sa-kai.
- ’Yan ta’adda sun kashe sojojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa a Abuja
- ’Yan bindiga sun sace mutum 36 a unguwar Keke a Kaduna
- An gano sabon samfurin cutar Maleriya a Arewacin Najeriya
“Duk buhunhunan da suka zo da su sai da suka cika su da wayoyi da duk abin da suka sata, saboda sai da suka far wa wajen gida 70”, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa “wannan ce matsalar da ke addabar mu yanzu, duka ta hana mu sukuni, ba dare da rana; Muna bukatar taimako na gaggawa a unguwar nan”.
Wani mazaunin unguwar mai suna Malam Aminu ya sanar da Aminiya cewa ’yan daban sun yi zuga ne su fiye da 50, inda suka far wa yankin da dare, suka kuma dinga buga gidaje suna sata da suka.
“Ni ma sun buga min gida amma na ki budewa, sai suka karya kofar suka shigo, suka dinga suka na a kai, amma dai Alhamdulillah ban mutu ba.
“Sai dai sun sace mana wayoyi da kudi da sauran abubuwan da ba za a rasa ba.”
SP Abdullahi Haruna Kiyawa dai shi ne kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, ya kuma ce tuni sun kamo mutane biyar, ciki har da wata mace, daga wadanda suka aikata ta’asar kuma sun amsa cewa suna cikin wadanda suka aikata laifin.
Ya cigaba da cewa: “tawaga ta musamman karkashin jagorancin SP Sani Garba Rijiyar Lemo, ta samu nasarar cafko wasu daga cikin wadanda ake zargi a yayin sintiri.
Kiyawa ya kuma ce bayan zurfafa bincike wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, tare da bayyana cewa sun dade suna addabar yankin na Kurna.