✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin Cocin Ondo: ’Yan sanda sun gano karin bama-bamai

Maharan sun yi shiga a matsayin masu ibada da a cocin

Babban Sufetan ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali ya ce an gano wasu bambamai da suka tashi ranar Lahadi a Cocin Katolika ta St Francis Xavier da ke garin Owo, Jihar Ondo.

Shugaban ’yan sandan ya yi Allah wadai da mummunan lamarin, in da ya ce maharan sun yi sojan gona ne a matsayin masu ibada a cocin.

“A binciken ’yan sanda suka gudanar sun gano ’yan bindigar  sun mamaye cocin ne da shiga irin ta mabiyan cocin, dauke da makamai da kuma abubuwan da ake zargin bama-bamai ne”, in ji shi.

“A bisa binciken ’yan sandan wadanda su ne tawaga ta farko da suka dira a wurin da lamarin ya faru bayan gano wasu harsasai na bindiga kirar AK-47;

“Sashen binciken makamai ya tabbatar da an yi amfani da bama-bamai a harin kuma ya gano burbushinsa a gurin da abin ya faru.

“Binciken rundunar ya kuma bayyana cewa wasu daga ’yan bindigar sun bad-da sawu a matsayin masu ibada a cocin daga bangarori daban-daban zuwa cikin cocin”, in ji babban Sifetan.

%d bloggers like this: