✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bam ya hallaka mutane a Kenya

Wadansu ’yan ta’adda  sun kai harin da ya hallaka mutum 14 a wani babban otel a Nairobi babban birnin kasar Kenya. Kungiyar Al-Shabab ta dauki…

Wadansu ’yan ta’adda  sun kai harin da ya hallaka mutum 14 a wani babban otel a Nairobi babban birnin kasar Kenya. Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin a otel din da ke Unguwar Westlands, inda suka kashe akalla mutum 14.

An jiyo karar harbe-harbe da fashewar abubuwa a cikin otel din na DusitD2 da ke Lardin Westlands da wasu ofisoshi ke ciki.

’Yan sanda sun kwashe mutane da dama cikin jini da harin ya rutsa da su. An kai harin ne da misalin kafe 12 na rana, inda  wani dan bindiga ya jefa kunshin bam a cikin wata mota da aka ajiye a harabar shiga otel din, daya kuma ya ta da bam din da ke jikinsa, kamar yadda Shugaban ’Yan sandan kasar Joseph Boinnet ya ce.

Wata mata da ke aiki a wani gini da ke makwabtaka da inda aka kai harin ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, “Kawai na soma jin karar harbe-harbe, can kuma na soma ganin mutane na gudu wadansu kuma na kokarin shiga cikin banki domin tsira da rayukansu.’’

’Yan sanda cikin gaggawa suka nufi inda aka kai harin. Daya daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa, “Abubuwa sun kazanta, mutane sun mutu.’’

Da misalin karfe 8 na dare kuma, ya ce  an tsaurara matakan tsaro a duk gine-ginen da ke yankin.

Bayan awa daya kuma, bayan an samu natsuwa, tare da zuba matakan tsaro a yankin, sai aka sake jiyo wani harbi duk da cewa Sakataren Harkokin Cikin Gidan kasar, Fred Matiang’i ya nuna cewa kura ta lafa kuma sun inganta tsaro.

Sannan ya ce, “Ta’addanci ba zai taba samun galaba a kanmu ba.’’

Mun murkushe ’yan ta’addan –Shugaba Kenyatta

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya ce an kawo karshen harin da ’yan ta’adda suka kai a Nairobi, kuma an kashe dukan ’yan ta’addan.

Jami’an tsaron kasar sun bayyana murkushe maharan awanni kadan bayan faruwarsa. Kuma duk da cewa Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin, ba a san mahara nawa ta tura ba.

A wani jawabi da ya yi wa kasar ta talabijin, Shugaba Kenyatta ya  ce maharan sun kashe mutum 14, kuma an kubutar da mutum 700.

Sai dai Kungiyar Agaji ta Red Cross ta ce mutanen da aka kashe sun kai 24.

A ’yan shekarun nan kasar Kenya tana yawan fuskantar hare-haren ta’addanci, musamman a yankunan da ke kusa da iyaka da kasar Somaliya da kuma babban birnin kasar.