Batun Baban-burin-huriyya
Batancin baragurbi na bibiya
Babatun masu kashin tsiya
Murmurewar moriyar murya
Barkanku ’ya’yan Bahaurobiya
Na ji ana ta surutai
Batutuwa barkatai
Babu mai nuna jinkai
Son kai ya tsananta sosai
Tattasai da tumatirin toye-toyen Turai
Murguda bakin cin kilishi
An kan ga gilashi
Ana ta yaren Ingilishi
An cokara cikon gashi
Baki ya ji dadin washi
Masu jibga jibar kashi
Wai an watsa musu tasshi
Har sun fara bin ba’asi
Wasu da suna wasi-wasi
Sun ji makogwaronka na amshi
An watsa musu garwashi
Tuwo suke jira a yi kwashi
Marar malmala kashi-kashi
Tabahuwa a biyata bashi
kar ta yi kisa a kowane sashi
Da an baza kiren karairayi
Kan tsananin laulayi
Wai Baba ya gaza furta uffan
Cewarsu ya bar batu kafatan
Ingarman karafa yai musu kayi
Harigidon hargowar harshe
Hanzarin hasashe
Tsunburburar Barbushe
Buzu da Bahaushe
Tuwo da miyar taushe
Barbaje
Baraje
Bambamin Bamaguje
Burungujin buje
Baje-baje
Hatsaniyar sassa
Hauhawar hawan sa
Hargowar harasa
Harsuna sun warwasa
Hawan-sa babu sa-in-sa
Hararagarken garaka
Harigidon garka
Hankoron hankaka
Haka-haka
Hayaniyar hauka
Hatsin hantsin hantsewa
Hawan-tsinin hautsinewa
Hadidiyar handamewa
Hankalin haukacewa
Hayagagar Haurobiyawa
Ayaga-ayaga
An yi yaga-yaga
An ja tunga
Na leka ta taga
Na fasko mahanga
A zo a yi jinga
’Yan wasa ai langa
’Yan kwadago ai gyaran danga
A daina duk wata burga
Zanzaron zawarawan zarga
Mangoro mai warin gawasa
Magaryar masu gasa
Marsa goriya raba wa sassa
Murhun miyar tafasa
Maburkin kada kubewa busassa
Gurgurar gwaggwabar garabasa
Gangamin gasa gurasa
Gungun gutsurar gullisuwa
Gatsar iloka da alewa
Gamayyar garuruwan kilisa
Kun ce nai yawan kaudi
Nakan kiyayi shaci-fadi
Zancena ya zamto gargadi
Abincina da nama mai dadi
Zumun zakwadin zumudi
Kwarmaton kwarankwatsa
Kwamacalar kwantsa
Kwankwatsa
kwatsa-kwatsa
kwalin kayan koli ya lotsa
In ka kai tumbatsa
Ka da kai batsa
Dinkin mahada da cunar hantsa
Mummunar manufa ka da ta ratsa
Kifi ya zam kamu a fatsa
Uwar dakan da aka kutsa
Abin da aka kitsa
Nonon saniya ya zam tatsa
Rike mana kaho mu matsa
Kowa ya tsaya ka da a motsa
Tsinin tsawon tsutsa
Tsallen tsanya ya runtsa
Tsinken tsakurar tsakuwa tsantsa
Tsarin tsaron tsatsa
Tsaya tsaf ka kimtsa
Ban da nunin yatsa
Balle ai bahallatsa
Komai ka guntsa
Yi dubin inda za ka watsa
Hakora a dumfari tuwon datsa
Gatsine gatsa-gatsa
Gungunin gumtsa
Gajalar gantsarewar gartsa
Gundumar gungun masu gyatsa
Gatarin gaftare gamjin gezar damatsa
Burgar burtuntunar Birtaniyawa
Farin cikin Faransawa
Jajircewar jinsin Jamusawa
Rausayawar rakashewar Rashawa
Amaren attajiran Amurkawa
Indira Gandhin Indiyawa
Janjamin jami’an Japanawa
Karafkiyar Koriyawa
Logar Larabcin Larabawa
Sansanin Sinawa
Kullin kudurin karfa-karfa kar
Kundunbalar kasar Katar
Karafunan hadin gwiwar nahiyar
Kaskantar da karamar kasa da kyar
Karajin kasashen tekun Pasha shar
Yamutsin Yamanawa
Sasarin Siriyawa
Turka-turkar Turkawa
Tattalin taliyar Italiyawa
Masar masarar Misirawa
Rugumniyar Romawa
Girkin Girkawa
Tattaunawar Turancin Turawa
Zomayen Zambiyawa
Zirga-zirga da zagayawa
Kalallame kalamai
Kamun bakin masu mukamai
Kai mai kame-kame
Ka sha damun dame-dame
Kantakaryar cin kudin makamai