Al’ummomin da ta’addancin ’yan bindiga ya shafa a Jihar Katsina, sun roki Gwamnatin Tarayya da ta fara samar musu matsuguni tukunna, kafin ba su duk wani tallafi.
Mutanen sun yi kiran ne a taron wayar da kai kan fara tattara bayanan wadanda ta’addanci ya shafa a jihar, wanda ma’aikatar jin kai da walwala ta kasa ta shirya.
Aminiya ta gano ma’aikatar ta fara aikin tattara bayanan ne a kananan hukumomin Batsari, Kurfi, da Jibia, da zummar sanya su cikin shirye-shiryenta na bada tallafi.
Shugabar jami’an ma’aikatar, Hajiya Nadia Muhammad Soso, ta bayyana a taron shi ne bakar wahalar da Gwamnatin Tarayya ta ga al’ummar na sha, da kuma bukatar samun wadanda za su kubuto da su daga kangin da suke ciki.
“Sanannen abu ne yadda rashin tsaro ke ci gaba da takaita hanyoyin samar da ababen more rayuwa ga mutanen da abin ya shafa da kuma a jihohin da lamarin ya faru.
“Don haka akwai bukatar samar musu da tallafin gaggawa da sauran taimakon jin kai”, in ji ta.