✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haramun ne gwamnati ta cire tallafin man fetur — Femi Falana

Lauyan ya kuma yi barazanar maka Gwamnatin a kotu kan gaza daidaita farashin man

Fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya ce bisa wani hukuncin Kotun Koli na shekarar 2009, haramun ne Gwamnatin Tarayya ta cire tallafi daga kowanne daga cikin albarkatun man fetur.

Lauyan ya kuma yi barazanar maka Gwamnatin a gaban kotu kan gaza daidaita farashin man fetur a Najeriya.

Ya ce watsin da gwamnatin ta yi da batun daidaita farashin ta bar dillalai na cin karensu ba babbaka ya saba wa hukuncin Kotun Kolin Najeriya.

Falana dai na mayar da martani ne ga kalaman Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timipre Sylva, yayin wani taron gabatar da nasarorin gwamnati mai ci daga 2015 zuwa yau, inda ya sanar da cewa an dade da cire tallafi a kan kananzir.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar da ranar Lahadi, lauyan ya ce a cikin wata shari’a tsakanin Bamidele Aturu da Ministan Man Fetur da kuma Babban Lauyan Gwamnati, mai lamba FHC/ABJ/CS/591/2009, Kotun Koli ta ayyana duk wani yunkuri na cire tallafi a matsayin haramtacce, wanda ba ya kan ka’ida kuma ya saba wa doka.

Ya kuma ce a lokacin, kotun ta umarci gwamnatin da kada ta kuskura ta yi watsi da daidaita farashin albarkatun man fetur, kamar yadda Dokar Man Fetur ta tanada, sannan ta rika wallafa farashinsa a kai a kai.

“La’akari da matsayin doka da wannan hukuncin da kotu ta yanke karara, ya nuna haramun ne gwamnati ta cire tallafi daga kowane nau’i na albarkatun man fetur.

“Yin hakan zai jefa ’yan Najeriya cikin matsin rayuwa idan aka ce an bar komai a hannun ’yan kasuwa.

“Muna kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya taka wa Minista Temipre Sylva birki kan raini ga umarnin Babbar Kotun Tarayya da kuma Kotun Koli a kan wannan batun,” in ji Femi Falana.