✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

….Har yanzu NFF ba ta samar masa matsuguni ba

Har yanzu Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ba ta cika alkawarin da ta yi na samar wa sabon kocin Super Eagles Grenot Rohr…

Har yanzu Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ba ta cika alkawarin da ta yi na samar wa sabon kocin Super Eagles Grenot Rohr masauki ba.
A yarjejeniyar da kocin ya kulla da NFF, an tanadar cewa hukumar za ta samar masa matsuguni ne a babban birnin Tarayya, Abuja.
Sabon kocin wanda yanzu haka yake Najeriya a kokarin tunkarar wasansa na farko a gobe Asabar a garin Uyo, an nuna zai koma Faransa ne da zarar an kammala wasan, saboda rashin takamaiman masauki.
Kocin ya ce yana sa rai Hukumar NFF za ta gaggauta samar masa masauki a Abuja don ya samu natsuwa a kokarinsa na  zakulo matasan ’yan kwallo da ke sassan Najeriya da ma wadanda ke kasashen waje. Kocin ya bayyana niyyarsa ta karade lungu da sakon da ke kasar nan don zakulo zaratan ’yan kwallon da za su kare martabar Najeriya.