Bayan makala ta ranar 26 ga watan da ya gabata mai taken Haba Kakaki kamar ba a Kaduna kake zaune ba?, wanda wannan jaridar da kuma Leadership Hausa suka wallafa a zaman martanina a kan makalar Malam Babangida Kakaki ta ranar 19 ga watan na Yunin, mai taken Gidan Rediyon FRCN: Ladan Salihu a Sikeli. Na ga kuma Malam Kakaki, ya sake wani rubutun mai taken Martani ga Ado Saleh Kankiya: Ladan Salihu ba shi da laifi. Wanda jaridar Leadership Hausa ta sake bugawa, har shafi daya da rabi, inda ya kara yin bincike akan abubuwan da na zargi Malam Ladan Salihu da aikatawa tun yana Daraktan Shiyya na tashar Rediyon FRCN da ke Kaduna,kafin ya samu matsawa gaba a zaman Darakta Janar na kulliyar gidajen Rediyoyin FRCN na kasa baki daya.
A wannan karon Malam Kakaki, ya yi kokarin ya ce lalle sai a raba dukkan abubuwan da Malam Ladan ya aikata a zamansa na Kaduna da wadanda ya yi ko yake yi yanzu a Abuja. Alhali Malam Kakaki ya san cewa ai zaman Malam Ladan na Kaduna shi ya sa da ya samu karin girma ya yiwa wadancan ma`aikata uku korar kare, korar da Malam Kakaki ya tabbatar an yi bisa ga hujjojin da ya bayar. Ke nan da bai zauna Kaduna ba, da wasu abubuwa na aiki ba su hada shi da wadancan ma`aikata ba, bare ya ya yi musu bita da kullin da ake zargin ya yi masu yanzu.
Ina mamakin Malam Kakaki da ya ke kokarin ya raba nasara ko rashin nasaran Malam Ladan akan zamansa na Kaduna da kuma na yanzu na Abuja, ko ya manta cewar zaman sa Kaduna, shi ya yi mujazar bita da kullin da ya kewa `yan lelen Malam Yusuf Nuhu (kamar Kakaki ya bayyanasu). Wadanda laifinsu ga Malam Ladan bai wuce zaman lafiyar da suka yi da Malam Yusuf Nuhu, alhali ya manta irin wancan zama har auratayya yana jazawa. Ina ga a kan haka Malam Ladan yana bukatar natsuwa ya kara yadda ake zamantakewa.
Kafin na yi nisa ya kamata Malam Kakaki da ire-irensa su san ina da alaka mai karfi da tashar FRCN Kaduna tun shekarar 1971, da na kama aiki da Madaba`ar Gwamnatin tsohuwar Jihar Arewa ta tsakiya da ke Kaduna (jihar da a yau ta kunshi jihohin Kaduna da Katsina) kusa da tashar FRCN Kaduna ta yau, har ta kai a shekarar 1981, da na samu aikin jarida da Kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya ta fi Kwabo dangantaka ta kara dinkewa sosai da sosai, da ta ma zama ta amintaka da manya da kananan ma`aikatan tashar. Ina son Malam Kakaki, ya sani cewa wannan dangantaka ta sanya a shekarar 2012, da FRCN Kaduna ta yi bikin cika shekaru 50, da kafuwa (1962 zuwa 2012), har rubutu na yi akan tashar. A wancan rubutu da aka buga a wannan shafi na bi sahun tarihin kafuwar tashar da irin zarar da ta yi wa tsara a aikin yada labarai, da kuma irin yadda ta tabarbare mummunar tabarbarewa a lokacin mulkin Malam Ladan. Ke nan Malam Kakaki ya sani ba yau na fara wannan rubutu ba akan tashar.
Amma shi Malam Kakaki mamakin shi ni ke, don ban san da wane lokaci suka shirya da Malam Ladan ba, har yanzu ya dage yana tallarsa haka. Don na san a cikin watan Oktoban 2009,lokacin Malam Kakaki yana Wakilin jaridar Leadership a Kaduna, ya yi wani labarin fallasa (ba fallasa ba ce haka ya kamata aikin ya zama) ta zargin wata badakalar yin sama da fadi da wasu makudan kudin tallar shirin gwamnatin Jihar Katsina mai lakabin Gaba dai gaba dai Jihar Katsina, badakalar, da har ta kai, bisa zargi mai karfi da akai wa Malam Ladan yana da hannu a ciki, ta sanya aka dakatar da shi har tsawon wata takwas. Wanda da aiki ake na wancan zamanin da dole Malam Ladan sai ya yi zaman sarka.
kokarin ya kare kansa daga matsin lambar jami`an gwamnatin Katsina akan waccan bakala, ta sanya Malam Ladan ya gayyato `yan sanda dauke da bindigogi suka kutsa kai cikin dakin watsa shirye-shiryen tashar ta Kaduna a cikin watan Oktoban 2009, inda `yan sandan suka tilasta wa mai gabatar da shirye-shiryen da lalle sai ya sanya wancan shiri na gwamnatin Katsina, alhali a lokaci badakalar ta bayyana, har Malam Yusuf Nuhu a zamansa na Darakta Janar na FRCN a Abuja ya turo da umarnin a dai na sa shirin ta hannun Malam Ladan ya kuma aika da kofen wasikar ga Mukaddashin Daraktan shirye-shirye Malam Sani Gwarzo, wanda cikin kokarin aiwatar da umarnin hakan ta faru, wannan badakalar na cewa Malam Kakaki ya yi rahoto akan ta lokacin yana Wakilin jaridun Leadership a Kaduna. Mai neman karin bayani akan kutsen `yan sandan a tashar ta FRCN Kaduna, sai ya duba kafar sadarwar intanet ta FRCN Kaduna, ya sha labari.
Ko kusa a wannan karon ba na son waiwayr batutuwan da Malam Kakaki ya dage akai na Malam Ladan dai hana jam`iyyar APC da `yan takararta irin su shugaban kasa da gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufa’i da reshen jam`iyyar na jihar Katsina da batun ya gyara dakunan watsa shirye-shirye na tashar Abuja har 22, domin, dukkan wadannan batutuwa wadanda suka shafa sun san an yi su kuma lokaci kadai suke jira, su san yadda za su da kujerar Malam Ladan. Don haka zan mayar da hankali ne akan wadancan mutane uku da Malam Ladan ya yi sanadin raba su da iyalansu hanyar cin abincin, inda ya sa akai musu korar kare ba garatute bare fansho, ga kuma nauye-nauye ya yi musu yawa kuma karfi ya kare masu.
Mai karatu ya san cewa a duk tsawon makalata ta farko, wadda kanunta suke jan hankali ga Malam Kakaki ko kusa ba inda nace su Malam Abubakar Abdurrahaman da Malam Haruna Aliyu Hadejia da kuma Malam Falalu ba su da laifi, amma na ce laifuffukan da suka yi laifuffuka ne da za a iya warware su cikin ruwan sanya kuma har yanzu ina kan baka na. Idan Malam Kakaki bai sani ba, Ni, na san ma`aikatan gwamnatoci da dama da aka kama da laifuffukan kin zuwa wurin aiki ko ma sata, amma adalcin shugaba ya sa aka ba irin wadancan ma`aikata shawara su ajiye ayyukansu aka kuma ba su kudaden sallamarsu suka kuma ci gaba da karbar fanshonsu, amma Malam Ladan bai samu zuciyar ya tausaya musu ba. Alhali shi a baya an zarge shi da laifin abin da ya fi nasu, aka yafe masa ya dawo bakin aikinsa, bayan wata takwas, yana da kace amma shi ya kasa tausaya musu, don kawai `yan lelen Malam Yusuf Nuhu ne.
Malam Kakaki ya ce wai Hukumar Daraktocin FRCN ta kori wadancan mutane, bisa ga matsayin albashinsu, ba Malam Ladan ba. Amma ya ki ya fadi cewa Malam Ladan mamba ne a cikin Hukumar, kuma ai shi ya shirya korar ya kai gabanta. A lokacin da takardunsu ya shirya ya kai gaban Hukumar ya ce a yi masu karin girma, yi masu za ta yi, ba tare da wata hiyana ba. Ya ci kuma a ce Malam Ladan ya kai matukar kurewa wajen bin dokokin koran ma`aikaci musamman irin wanda ya samu irin wadancan shekaru, sannan kuma ya tausaya, amma duk bai yi ba, don kawai wadanda ake tuhuma `yan lelen Malam Yusuf ne.
Maganar kudaden tafsiri a Jihar Zamfara da ka yi zargin Malam Abubakar ya cinye, har an gurfanar da shi gaban kuliya. Ni abin da naji labari, shi ne Hukumar FRCN Kaduna ta ba da takaradar tuhuma ga Abubakar ya kuma amsa, kuma ba ta kara cewa da shi kome ba. Batun maganar tana kotu ban san gaskiyar haka ba, amma dai na san abu daya kuma dukkan ma`aikacin Rediyo FRCN Kaduna kai har ma na Abuja da mu abokan aiki, an san Malam Abubakar da kokarin kamanta gaskiya da rikon amana da kokarin kaucewa aikata ba daidai bayan jajircewa wajen aiki. Ko shi ma Malam Ladan haka yake?
Mai son cikakken wannan makala sai ya tara a jaridar Leadership Hausa ta wannan makon, in Allah Ya so, anan r ashin fili ba zai ba da damar in ci gaba ba. A sha ruwa lafiya.