✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu ba mu cimma matsaya da gwamnati ba —ASUU

Tsawon watanni kusan takwas kenan gwamnatin tarayya da kungiyar malaman Jami'o'i ASUU sun kasa kawo karshen yajin-aikin da kungiyar ta shiga.

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce kawo yanzu babu wata matsaya da ta cimma da Gwamnatin Tarayya domin kawo karshen yajin aikin wata bakwai da ta shiga. 

Hakan ya fita ne daga bakin shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, inda ya ce babu wata bukata tasu da aka biya.

“Kamar yadda muka sani babu wata bukata da aka cika wa ’yan kungiyar, don haka ba za mu yarda da alkawarin bogi ba.

“Albashin wata hudu zuwa takwas da wasu alawus-alawus da aka rike har yanzu ba wanda aka biya.

“Yarjejeniyar da aka yi a 2009 ba a cika mana ba, ballanta a fara maganar alkawuran 2019, wanda ko kansu ba a zo ba.

“A shirya muke a duk lokacin da suke bukata a zo zauna a tattauna,” inji Ogunyemi.

Yajin aikin da malaman jami’o’in suka shiga ya dauki tsawon kusan wata takwas ba tare da sun cimma matsaya da gwamnati ba.

Sai dai wasu na ganin kowanne daga bangarorin gwamnatin da ASUU na da irin rawar da zai iya takawa wajen ganin an kawo karshen yajin aikin.