Kimanin shekaru bakwai bayan kafuwar jam’iyyar APC mai mulki, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce har yanzu jami’yyar ba ta zama tsintiya madaurinki daya ba.
Gwamnan ya bayyana APC a matsayin ‘hatsin bara’ wacce har yanzu jami’yyun da suka hadu domin kafa ta ke fafutukar zama wuri guda.
- Rasha: Putin ya sa hannu kan dokar da zai yi mulki har 2036
- ‘Za mu fasa shagunan ’yan kasuwar da ke boye kayan masarufi a Kano’
Ganduje ya yi wadannan kalamai ne a Kano, yayin wani taron jin ra’ayin jama’a da Kwamitin Yi wa Kundin Tsarin Mulkin APC Garambawul shiyyar jihohin Arewa maso Yamma ya shirya ranar Litinin.
Ya ce, “APC ta fara ne a matsayin gamayyar jam’iyyun ACN da ANPP da APGA da PDP da CPC…wannan gamin gambiza ne da ke kokarin narkewa su zama abu daya.
“Sai dai abin takaici, har yanzu tsawon wadannan shekarun APC ba ta dunkule ta zama daya ba.
“Wadanda suka karanci Kimiyyar Harhada Sinadarai [Chemistry] sun san bambancin gamin gambiza da dunkulallen abu.
“Duk abin da aka kira shi da gamin gambiza, to za ka iya raba shi cikin sauki, abin da ya dunkule kuwa, da wahala a iya raba shi, kuma ko da ka cire wani bangare na jikinsa babu abin da zai samu da shi,” inji Gwamnan.
Sai dai ya bayyana kwarin gwiwa cewa taron jin ra’ayoyin jama’ar zai magance wannan kalubalen har jam’iyyar ta zama dunkulalliya.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Garambawul din na APC shiyyar Arewa maso Yamma, Dakta Tahir Mamman ya ce dole ne duk abin da ya kafu na tsawon shekaru bakwai zuwa takwas ya fuskanci kalubale iri-iri, inda ya ce taron ya zo a daidai lokacin da ake bukata.
Mamman ya kuma ce taron wanda ya tattaro dukkan shugabannin jam’iyyar na jihohin yankin zai taimaka wajen sake hada kan ’ya’yanta domin ta ci gaba da rike madafun iko har tsawon shekaru 32 da suka yi harsashe ko ma fiya da haka.
Aminiya ta gano cewa wakilan jihohin guda bakwai sun gabatar da shawarwarinsu ga kwamitin ya mika wa uwar jam’aiyyar ta kasa domin aiwatarwa.