✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin tafiyar da gamin gambizar Sha’awa (3)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan hanyoyin tafiyar da gamin gambizar sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya, da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.

Hanya 3: Tattaunawa

Budaddiyar kafar sadarwa tsakanin ma’aurata rigakafi ne na hana bullar kowace irin matsala cikin rayuwar aurensu, in kuma har ta bulla, to nan da nan za su magance ta. Yawanci ma’aurata za su tattauna game da kowane bangare na rayuwarsu, amma ban da bangaren sha’warsu ko ibadar aurensu, alhalin shi ne mafi muhimmancin sama da komai a rayuwarsu, shi ne abin da su kadai ke da shi ba mai yi masu tarayya a cikin mallakarsa. Duk dayan da ke da matsalar sha’awa ko ta ibadar aure daga cikin ma’aurata to wajibi ne ya sanar da dayan, cikin hanya mafi dacewa kuma cikin salsalar magana mai kyau ba tare da mita ko zargi a ciki ba, sai ya fadi duk abin da ke damunsa ko irin abubuwan da yake so wanda dan’uwan aurensa ba ya yi masa su, kuma duk wanda ya ji bukatun dan uwansa, to kada ya raina su ko ya yi masu mummunar fassara, sai dai ya dage wajen ganin ya yi wa dan uwan aurensa gwargwadon iyakar iyawarsa, mu tuna so da kauna dole sai da sadaukarwa, rashin sadaukarwa alama ce ta cewa akwai wani rauni cikin soyayyar da ke tsakanin ma’aurata.

Yawanci mata na zama cikin rayuwar kunci a gidan aurensu saboda kunya! Ba sa iya sanar da mazajensu irin bukatunsu na sha’awa ko yanayin ibadar aure, to wannan irin kunyar ba ta da amfani a cikin rayuwarki ya ’yar uwa! Tun da kullum sai dai ta yi ta kara nutsar da ke cikin kunci da halin kaka -ni- ka- yi. Amma ga wacce tsananin kunyar ya hana ta sanar da mijinta bukatunta ko irin halin da take ciki dalilin ibadar aurensu, tana iya rubutawa a rubuce ta ba maigidanta, kai kuma maigida sai ka dage ka zama cikakken maigidan in ka karanta.

Haka kuma maigida da uwargida na iya zama lokaci daya kowannen su ya jeranta abubuwan da yake so da wadanda bai so a rubuce game da ibadar aurensu (ko ma yanayin zamantakewarsu), sai su bai wa juna, wannan zai taimaka masu wajen gyara kurakuran da suke yi wajen ibadar aure, kuma zai sa su gane abubuwan da za su rika yi don faranta wa juna lokacin ibadar aure.

Hanya Ta 4: Maigida Ya Zama Cikakken Namiji:

Maigida, ka sani kuma ka rika tunawa kodayaushe cewa kai ne fa Maigidan! Kai ke jan ragamar gidan, da Uwargidan da gidan duk karkashinka suke. Komai irin murdewar halayyar Uwargida ko irin nauyin sha’awarta, in Maigida ya gane sirrin da ke cikin aiwatar da dukkan fasahohi da kuzarorin namijintakarsa, to zai iya tafiyar da Uwargidarsa yadda yake so kuma zai iya zakulo daskararriyar sha’awarta waje. Ba macen da ba ta da sha’awa, sai dai dole akwai wasu mabudai da ake amfani da su don bankado da sha’awar daga cikin jikin ta har ta bayyana. Ga magidanta da ke ganin kamar matansu ba su da sha’awa to mabudan da suke amfani da su ba su yi daidai da irin kofofin sha’awar matan su, ba shi ya sa.

Zama cikakken namiji ba wai kawai a yi ta ji da mace ba ne ta hanyar yi mata duk abin da take so da guje wa abubuwan da ba ta so ba, zama cikakken namiji shi ne amfani da wannan karfin hankali, karfin hangen nesan da karfin kuzarin nan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ba maza sama da mata wajen aiwatar da kowane bangare na rayuwar aure. Mace na jin dadi da samun kwanciyar hankali in har ta tabbatar da cewar mijinta cikakken namiji ne ta kowane bangare na rayuwa, wannan jin dadi da kwanciyar hankalin kuwa shi ne mabudin babbar kofar sha’awar ’ya mace.

Sannan mu tuna da fadin Manzon Mu SAW ga Magidanta: “Mafi alherin cikinku su ne mafiya kyautatawa ga matan su” don haka magidanta masu sa tsauraran matakai ga matansu da ka’idoji masu takurawa ga matansu, to ku sani namijintakar ku ta yi rauni saboda haka sai ku gyara halayen ku. Abu mafi dacewa shi ne fahimtar Uwargida da fahimtar yanayin halayyarta sai a sa mata dokoki daidai da ita, duk wata dokar da za ka sa wa matarka, komai alfanun ta, in dai wannan doka ta zama mai tsananin takura wa ce gareta, to fa a hankali son ka zai yi ta raguwa cikin zuciyarta, ga ’ya mace kuwa, in ba so, to ba sha’awa!

Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.