✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi biyar na magance matsalolin fata

Fata tana da muhimmanci a jikin mutum don haka bai kamata a yi sakaci wajen kulawa da ita ba. Kafin a gano kyawun mutum sai…

Fata tana da muhimmanci a jikin mutum don haka bai kamata a yi sakaci wajen kulawa da ita ba. Kafin a gano kyawun mutum sai an fara gano yanayin fatarsa tukun. Kuma kafin a san cewa mutum yana cikin jin dadi ta fata ake ganewa. A wannan hanyoyin za a koyi yadda za a magance cizon kudin cizo a fata da sauransu. Akwai man shafawa nau’i-nau’i da muhimmi ne wajen amfani da su domin inganta fatarmu, kamar man kwakwa da man lemun tsami da man zaitun da na fiya da  sauransu.
•    kurajen fuska: Domin magance kurajen fuska, za a iya amfani da zuma mai kyau, a shafa ta a tafukan hannu sannan a shafa ta a fuska kamar yadda ake shafa man shafawa. A jira na tsawon mintuna 10 zuwa 15 sannan a wanke. Idan ana hakan a kullum lallai za a rabu da kurajen fuska.
•    kurajen fatar jiki; a samu man lemun tsami da man kwakwa sannan a kwaba su sai a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta samu matsala.
•     Domin cizon kudin cizo :  A samu man ‘argan’ ( za a iya samu a manyan shaguna da ke sayar da kayan kwalliya) a rika digawa a wajen cizon safe da yamma. Za a ga alamar cizon ya bata har wajen ya warke.
•    Fatar labba:  Yanzu lokaci ne da ya kamata mu kula da fatar labbanmu saboda sanyi. A samu zuma da sukari a kwaba su, sai a shafa  a kan leben, sai a wanke a shafa man kwakwa ko zaitun a lebben.
•    kankara na hana fesowar sababbin kuraje a fuska. A samu kankara a rika shafawa a fuska na tsawon minti biyar zuwa 10 a fuska akalla sau daya a rana. Yin hakan na hana haifar da kuraje a fuska.