✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi 15 da za ka sa matarka cikin farin ciki

1.      Idan ka shiga gida  ka ce Assalamu alaikum’ shaidan zai bar gidan!2.      Ka rika yawan ba ta labarai. Saboda Allah (SWT) Ya…

1.      Idan ka shiga gida  ka ce Assalamu alaikum’ shaidan zai bar gidan!
2.      Ka rika yawan ba ta labarai. Saboda Allah (SWT) Ya sanar da mu cewa dan Adam yana son jin labari.
3.      Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kushe ta ka nuna bacin ranka.
4.      Ka zama mai yawan ba ta kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya.
5.      Ka share wasu daga cikin kura-kurenta. Ka nuna ba ka ma san ta yi ba. Kuma ka dauke shi a matsayin abin da ya shude, kada ka ajiye shi a kwakwalwarka.
6.     Ka nuna mata tausayawarka gare ta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al’ada.
7.    Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana’a sama da matansu).
8.      Ka nuna mata babu wata budurwa da ke gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a wurinka.
9.      Ka rika tunawa da ita a cikin addu’arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku.
10.      Kada ka nuna mata cewa kana yi mata alfarma ne a kan wata hidima da kake yi mata, kamar sayen abinci, saboda dama hakkinta ne ka kawo mata, sannan ka sani cewa abincin kawai kake kawowa amma Allah Shi ne Mai ciyarwa.
11.      Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba.  Lokuta da dama idan mata da miji suka dan samu sabani har ta kai ana maida martani cikin fushi, to ka tuna ba daga ita ba ne, Shaidan ne ke zugata, saboda shi yana matukar son a yi saki.
12.      Ka dauki abinci ka sanya mata a baki. Annabi (SAW) ya ce, “abincin ba cikinta kadai zai shiga ba, zai wuce har  zuciyarta.”
13.      Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara’a domin Manzo (SAW) ya ce: “Duk wanda ya nuna wa matarsa fara’arsa, to daidai yake da yin sadaka.”
14.      Ka zama mai yawan neman shawararta. (Wasu suna ce wa ba a shawara da mata). To ku sani cewa Manzo (SAW) ya kasance yana shawara da matansa.
15.  Kada ka boye mata damuwarka, farin cikinka ko bakin cikinka domin ita magani ce a tattare da kai.