✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hancina na nan?

Akwai wani dattijo da mura ta sako shi a gaba, hancinsa na ta yoyon majina. Sai ya tafi wani kanti kusa da shi don ya…

Akwai wani dattijo da mura ta sako shi a gaba, hancinsa na ta yoyon majina. Sai ya tafi wani kanti kusa da shi don ya sayi Robb ya shafa. Da ya isa kantin ya ce a ba shi Robb, sai mai kanti ya ce babu, ya tambayi Mistaleta, aka ce babu. Mai kanti ya ce Loko kawai yake da shi, amma yana da zafi sosai.
Dattijo ya ce wane zafi ne lokacin Yakin Basasa ba su gani ba, har barkono mai sa hawaye suke shaka. Mai kanti ya ba shi Loko. Dattijo ya ba shi Naira 500 a ba shi canji, mai kanti yana neman canji. Sai dattijo ya lakaci Loko ya sanya a kofar hancinsa daya, ya kara lakata ya sa a dayan.
Kafin mai kanti ya ba shi canji sai dattijo ya shiga tsalle, saboda tsabar radadi.
Mai kanti na kokarin ba shi canji sai ya ji dattijo ya ce: “Hancina na nan?” Mai kanti ya ce masa yana nan mana. Sai dattijo ya ce,  “Amma yana fesar da wuta ko?” Mai kanti ya fashe da dariya, sannan ya ce masa, a’a.
Bashir Musa Liman, 07036925654