✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana shigowa da motoci ta kasa alheri ne – Rabi’u Katuru

  Biyo bayan dokar da gwamnatin tarayya ta yi na hana shigo da motoci ta kan iyakar kasa, da za ta fara aiki daga ranar…

 

Biyo bayan dokar da gwamnatin tarayya ta yi na hana shigo da motoci ta kan iyakar kasa, da za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa, al’ummar kasar da masu hada-hadar motoci a Najeriya ke ta bayyana ra’ayin su bisa matakin gwamtin..

Alhaji Muhammadu Rabi’u Katuru shugaban kamfanin Dillancin motoci na Katuru motors da ke Legas, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki a kasar nan a yanzu hana shigowa da motoci ta kan iyakar kasa ba shi ne mafi alfanu ga kasuwar hada-hadar motocin ba, abin da ya fi shi ne a farfado da darajar Naira, domin a halin da ake ciki yanzu kasuwar hada-hadar motocin na daf da durkufewa a kasar, sakamakon yanayin tabarbarewar tattalin arziki, inda a yanzu mafi yawan dilallan motoci a kasar nan ba sa iya zuwa kasashen waje su saro mota, sakamakon karyewar darajar Naira.
“A shekarun baya a duk wata nakan je kasar Amurka in shigo da kwantaina hudu zuwa shida na motoci, amma a yanzu yau sama da shekara daya da rabi ke nan ba na iya fita in sayo. Motocin da nake da su a baya su nake sayarwa, kuma suna daf da karewa ba kuma zan iya dibar kudi in je sayen wasu ba, saboda lalacewar darajar Naira. Idan an sayo ma babu wata riba, sai dai asara,” inji shi.
A cewar Alhaji Rabi’u Katuru, matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana shigowa da motoci ta bodar kasa alheri ne, domin kamata ya yi a ce ana sauke motoci kai tsaye ne daga Amurka da sauran kasashen Turai zuwa Najeriya ba tare da an kai su kasar Benin ko Nijar ba. Don hakan ne zai bai wa Najeriya damar samun cikakkun kudin shiga, kuma ta haka ne ‘yan Najeriya za su amfana da lafiyayyun motoci da ba su da aibi ko hadari.
“Yau sama da shekaru 12 ke nan nake harkar saye da sayar da motoci, kuma tun fil azal ta ruwa nake shigowa da kayana, ba na kawowa ta Kwatano, don ba ma son duk wani abin da zai taba lafiyar motocin da muke sayowa, sai dai akwai ‘yan uwanmu, abokan harkar da su ta kasa suke shigowa da nasu, musamman masu karamin karfi, wadanda ke sayan uku ko biyu ko daidai don a kan samu saukin Naira dubu 150. Hakazalika mafi yawan masu shigowa da kananan motoci ta kasa suke shigowa da su, to amma idan matakin da gwamnatin ta dauka zai zamo mana alheri sai mu cigaba da addu’a, domin a zahiri mataki ne da zai bunkasa kudin shigar gwamnati, kuma al’umma su samu tabbacin sayen ingantattun motoci, amma muddin aka rufe kan iyakar kasa a yanzu, mutane da yawa sai dai su dinga dabawa a sayyada, suna takawa a ƙasa. Don mutum da kudinsa sai ya rasa motar saya, ko kuma a koma sayen tsofaffin motocin da aka hau su a nan gida. Domin ko a yanzu ma mutane da yawa na fitar da motocin hawan su suna sayarwa don ba tasu ake ba, ana neman abin da za a sanya a baka ne,” inji shi.
Shugaban kamfanin dillancin motocin na Katuru motors ya ce a yanzu mafi yawan dilallan motoci ba sa iya zuwa kasashen waje su saro mota, saboda tashin gwauron zabi da Dala ke cigaba da yi.
Ya ce babu yadda dillali zai sayi Dala a kan Naira 480 ya shigo da mota ya ci riba. Don haka a yanzu filayen da ake sauke motoci a bakin tashar ruwa na tsibirin tinkan a Legas sun koma tamkar wani filin ƙwallo don babu motocin. Don haka abin da dilallan motocin ke bukata a halin yanzu shi ne a bunkasa darajar Naira don su samu ikon cigaba da shigo da motocin ta ruwa, kamar yadda gwamnatin ke bukata.