✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin Kirista (2)

Almasihu ya ce “Kun dai ji an ce sakayyar ido ta ido ce, sakayyar hakori kuma ta hakori, amma ni ina gaya muku cewa  kada…

Almasihu ya ce “Kun dai ji an ce sakayyar ido ta ido ce, sakayyar hakori kuma ta hakori, amma ni ina gaya muku cewa  kada ku rama mugunta da mugunta, duk wanda ya mare ku a kuncin dama, ku juya masa daya kuncin, haka kuma idan wani ya yi kararku domin ya kwace muku mayafi, to ku mika masa taguwarku ma, duk kuma wanda ya tilasta muku tafiyar kilomita daya ku yi masa ta kilomita goma, ku ba wadanda suka roke ku, kada kuma ku hana duk wanda ke neman rance a wurinku.
Kun dai ji an ce ku kaunaci makwabcinku, ku kuma nuna kiyayya ga magabtanku, amma ni ina ce muku ku kaunaci makiyanku ku albarkaci wadanda ke zaginku, ku yi wa makiyanku alheri, sannan ku yi wa masu tsanata muku addu’a, domin ta haka ne za a kira ku da sunan ’ya’yan Allah Madaukakin Sarki, domin Yakan saukar da rana a kan mugaye da nagartattu, Ya kuma saukar da ruwan sama a kan masu gaskiya da marasa gaskiya. Domin idan wadanda ke kaunarku kadai kuke nuna wa alheri wane lada za ku samu? Ba daya kuke da sauran al’umma ke nan ba? Idan kuma dan uwanku kadai kuke gaidawa, me ke nan ya bambantaku da saura? Sauran al’umma ba su yin haka ne? Don haka sai ku kasance cikakku kamar yadda Ubanku da ke cikin sama Yake cikakke.” (Matta sura 5 aya 38).
A wannan wuri da muka karanta mun ga yadda Almasihu ke fadakar da almajiransa da mabiyansa, kuma idan muka yi nazari sosai za mu gano cewa babu wani abu da Almasihu ke fadakarwa a cikin wadannan ayoyi illa zaman lafiya a matsayin daya daga cikin irin halayensa.
Hakan na nuni da cewa duk Kiristan da ke tinkaho da sunan Almasihu kamata ya yi ya kasance mai hali irin na Almasihu ta hanyar yin biyayya da aiki da fadakarwarsa.
Ana bukatar Kirista ya nuna hakuri, sannan kada ya kasance daga cikin masu daukar fansa, maimakon haka ya tuna kalmar nan ta Ubangiji da ke cewa “Ramuwa tawace Ni kuma Zan saka.”
Haka kuma Almasihu bai tsaya nan ba, bayan ya fadakar da su sai kuma ya sake nuna musu a fili kamar yadda yake a rubuce cikin Littafi Mai tsarki (Baibul): “Da yake magana sai daya daga cikin sha biyun nan mai suna Yahuza ya zo tare da daruruwan mutane rike da takubba da sanduna daga wurin manyan Firistoci da dattawa da kuma manzanni, inda shi kuma mai bashewar ya nuna alama cewa wanda ku ga na sumbace shi shi ne mutumin, sai ku kama shi. Daga nan sai ya matso kusa da Almasihu ya ce ranka ya dade shugaba, sannan ya sumbace shi mutanen suka kama Almasihu, za su tafi sai daya daga cikin wadanda ke tare da Almasihu ya zare takobi ya kai sara har ya yi sa’ar dauke kunnen daya daga cikin mutanen da suka kama Almasihu. Ganin haka sai Almasihu ya gaggauta kwabar mutumin inda ya ce “Maida takobinka a cikin kube domin duk wanda ya zare takobi takobin ne ajalisa.” Ya kara da cewa “Kuna ganin ba ni da ikon yin addu’a ga Ubana da ke cikin sama don ya aiko min da rundunar Mala’iku? Amma idan na yi haka yaya annabcin zai cika, kan cewa hakan za ta faru? Daga nan sai Almasihu ya ce wa tawagar mutanen, kun fito rike da takubba da sanduna kamar za ku kama dan fashi da makami, na shafe lokuta ina fadakarwa a cikin haikalin da ke tsakaninku, amma ba ku iya kama ni ba, amma duk wadannan abubuwa sun faru ne domin a cika annabci kamar yadda Annabawa suka bayyana, sannan a take sai almajiransa suka watse.”(Matta sura 26 aya 47)
A wannan wuri da muka karanta mun ji matakin farko da Almasihu ya dauka na neman zaman lafiya da kaunar magabta kuma ya saka mugunta da alheri domin bayan da Almasihu ya kwabi daya daga cikin mabiyansa da ya kai sarar da ta guntule kunnen daya daga cikin mutanen da suka zo don kama shi, sai ya taba bangaren kunnen da aka sare inda a nan take ya warke wurin ya koma tamkar babu wani abin da ya auku.(Luka sura 22 aya 51)
Almasihu ya fuskanci matsaloli da dama da suka hada da cin zarafi na ba gaira ba dalili da kaskanci da ba’a ko shakiyanci inda aka yi masa rawanin kaya sannan aka koma ga kiransa da sunan Sarki, an yayyage masa tufafi aka shimfida rigarsa a kasa aka yi caca a kanta.
Ba su tsaya nan ba, domin bayan da suka bada shaidar zur da ta sa aka yi wa Almasihu hukuncin kisa ta hanyar gicciyewa, sun kuma sanya shi a tsakiyar ’yan fashin da tuni suka amince da azabar da suke sha tunda sun san irin laifuffukan da suka tafka.
Amma duk wadannan abubuwa da suka auku da Almasihu bai yi wani tunanin daukar fansa ba, maimakon haka sai ya dauke su a matsayin wadanda ba su san abin da sukeyi ba, don haka babu wani abin da suke bukata illa addu’a, inda nan take ya ci gaba da rokon Allah Ya gafarta musu zunubansu.