✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Talatu Zainab Abdulmumin: Mace ba kamar namiji take ba

Hajiya Talatu Zainab Abdulmumin ita ce Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa (SSG), ta yi digirita na daya da na biyu a fannin koyarwa a jami’ar Jos,…

Hajiya Talatu Zainab AbdulmuminHajiya Talatu Zainab Abdulmumin ita ce Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa (SSG), ta yi digirita na daya da na biyu a fannin koyarwa a jami’ar Jos, ta bukaci mata su daina ganin kansu a matsayin maza, su kasance rikon amana da kamala da natsuwa da kuma gaskiya.

Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Talatu Zainab Abdulmumin. An haife ni a garin Nasarawa da ke karamar Hukumar Nasarawa, a Jihar Nasarawa a ranar 11 ga watan Afrilu, 1962. Na fara firamare a Central Primary School da ke cikin garin Nasarawa, inda na kammala a Township Primary School a Jos, Jihar Filato. Na yi sakandare a makarantar mata da ke garin Jos da ake kira Saint Peace College Jos. Na yi digiri na daya da na biyu a Jami’ar Jos. Na yi hidimar kasa daga 1986 zuwa 1987 a makarantar Koyar da Ungwanzoma (school of nurse) da ke garin Sakkwato, sai na samu aiki a jami’ar tarayya da ke garin Nasarawa watau bayan na koma gida ke nan. Na yi aiki a daga 1987 zuwa 2005 lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Abdullahi Adamu ya nada ni a matsayin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi, daga bisani na koma ma’aikatar wasanni da yawon shakatawa. Bayan Tanko Almakura ya zama Gwamnan Jihar Nasarawa sai aka sake mayar da ni ma’aikatar ilimi a matsayin Babbar Sakatariya. Matsayin da na rike kafin Allah cikin rahamarSa ya ba ni sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa (SSG).
Burina ina karama
Tun ina karama nake burin zama malama. Ba zan iya cewa ko don sha’awar yadda malamai ke koyarwa ko don mahaifina malami ba ne. Mahaifina na daya daga cikin tsofaffin da suka fara karatun boko a wurinmu, bayan ya kammala karatunsa ya fara koyarwa. Ka ga na fito daga gidan malamai. To hakan ne ya sa bayan na je jami’a na zabi fannin koyarwa. Na karanta Turanci (English). Digirina farko da na biyu a fannin koyarwa ne. Kodayake burina ya cika tun da na yi rajista da hukumar malaman Najeriya (Teachers registration Council of Nigeria).
Halayen da na koya a wurin iyayena ina karama
A gaskiya abin da na koya wurin iyayena su ne hakuri da juriya. A duk halin da ka tsinci kanka sai ka yi tawakkali da Allah ne mai bayarwa ga wadda Ya so, hakan ya sanya na tashi cikin wadatar zuci, domin tun da muka fara karatu har ga neman aiki da sauransu babu wanda zai gaya maka yau cewa mahaifinmu ya je nema mana alfarma, bai yi haka ba don ya tabbata hazaka da kazo ne za su ba da abin da ya dace da rayuwa. Ya karfafa mu ya kuma ba mu goyon baya. Shi ya sa dukanmu muka yi karatun boko; duk da cewar mun fi goma a wurin babanmu. Kuma a cikin rahamar Ubangiji mun yi digiri. Wasu ma suna da digiri na biyu wasu fiye da haka, kuma dukanmu muna aiki. A cikin ayyukan da muke yi mahaifinmu bai taba ce ko sau daya bari in ba da cin hanci don a kara wa ‘ya’yana matsayi ba. Yakan bar mu ne mu yi amfani da kwakwalwarmu wajen neman na kanmu. Ka ga kamar abin da ke faruwa yau, za ka ga za an bi ta bayan fage don a nema wa yaro aiki ko wani abu makamancin haka. Mahaifinmu ya yi ta mana huduba cewa idan har ka yi hukuri da abin da Allah Ya ba ka, to babu shakka rayuwarka za ta zama ingantacciya. Za ka ga ba ka da matsala wurin mu’ammalarka da jama’a don ba ka sa kwadayi ciki ba. Shi ya sa a duk inda muke kuma duk aikin da muke yi mahaifinmu yakan gaya mana cewa mu sa sa ido a kan kudin jama’a, mu yi taka tsan-tsan mu ji tsoron Allah.  Mahaifina da nake maka bayyani a kansa watau Alhaji Ahmadu Tanko shi ya fara bude ma’aikatar ma’aikatan Jihar Nasarawa (cibil serbice commission). Ya kuma ba da tsarin yadda za a gudanar da harkokin ma’aikatar wannan jiha a fanni horo (discipline) da dai sauransu. Haka ne ma ya sa yau idan ka ji ana ba da tarihin ma’aikatan wannan jiha, za ka ji ana ai lokacin baba haka ake kiransa, an yi kaza; an yi kaza. To ka ga ba shakka ya kawo ci gaba sosai a wajen horon ma’aikatan Jihar Nasarawa baki daya.

Nasarori      
To ni dai ba zan bayyana maka nasarori da na cim ma a rayuwa ba, don ina sadaukar da rayuwata ne wajen yi wa jama’a aiki. Saboda haka wadanda nake yin aiki domin su ne zan so a ce sun bayyana nasarori da na cim ma a halin yanzu. Su ya kamata su san ko na taka mahimmiyar rawa a rayuwarsu ko a’a. Babban abin da ni dai nake gani na samu nasara a kansa sosai shi ne, cikakken goyon baya da nake ba Gwamna Almakura don ba shi damar aiwatar da abin da aka zabe shi ya yi. Ina ba shi goyon baya ne don tabbatar da cewa abin da ya dace a yi wa jama’a an yi shi. Kuma na samu nasarar yin haka ba wai yabon kai ba. Sauran nasarori kuma kamar yadda na bayyana maka jama’a da nake yin aiki dominsu ne ya kamata su bayyana. Musamman ka ga wannan ofis dina shi ne ke aiwatar da abubuwa da gwamnati ta ce a yi. Ni kuma ina tabbatarwa an yi din. Saboda haka ko na ci nasara ko ban ci ba jama’a ne ya kamata su zama alkalai.
Abin da nake so a tuna ni da shi
To, ni dai kamar yadda na bayyana maka a baya ina sadaukar da lokacina da komai da nake da shi ne wajen yi wa jama’a aiki. Abin da zan so a tuna da ni idan ba na nan shi ne – mace wadda ta taimaka wa jama’a sosai don cim ma burinsu a rayuwa. Ta kuma kawo ci gaba mai dorewa a Jihar Nasarawa da ma kasa baki daya.
Wuraren da nake sha’awar zuwa lokacin hutu
 To, ni ma kamar kowace ’ya Musulma, ba inda nake sha’awar zuwa a duniya a kowane lokaci kamar Saudiyya. Ka ga na farko za ka je ne ka ga abin sha’awa; na biyu kuma ibada. Domin idan kana wajen tamkar kana gaban Allah (SWT) ne. Duk wani abin duniya ka aje gefe guda ka fuskanci Ubangiji. Saboda haka babu inda nake son zuwa kamar Saudiya. Idan kuma a gida ne nan Najeriya ba inda nake son hutu kamar tare da iyayena don har yanzu suna da rai. Nakan je can garinmu Nasarawa in yi hutu da su suna ba ni shawarwari. Domin har yanzu ni ‘yarsu ce. Kuma har yanzu tun da suna da rai, ina burin kasancewa tare da su kullum don tsintar wasu abubuwa da za su gyara mini rayuwa.
Halayen  da ke burge ni   
Watau halaye masu kyau su ne sanin ya kamata da rikon amana da gaskiya. Domin Allah (SWT) Ya ba mu mata wasu umurni da suka zamanto cikamaki ga halayen maza. Ka ga bai dace mace ta rika ganin kanta kamar ita ce namiji ba. Domin kowa Allah Ya ba shi umurni. Saboda haka ina so in ga mace mai natsuwa mai sanin ya kamata mai kuma ladabi da biyayya, idan aka ce bari sai ta bari. Kada a samu mace ta zama fitinanniya. Ina so mace mai son zaman lafiya a duk yadda ta samu kanta, domin ita uwa ce komai kankantarta kuwa. Ya kamata ta zama uwa ta zama kanwa ta kuma zama ‘ya. Ba ta rika tayar da zaune tsaye ba. Idan ana hayaniya ma idan kina wurin a matsayinki na mace ana so ki kashe wutar rikicin ne, watau ki kasance mai sasantawa. Shi ya sa sau da yawa nakan kasance cikin bakin ciki in ga mata suna bangar siyasa. Wannan ba halin mace ba ne domin mace an san ta ne da kamala. Ba a ce kada ta yi siyasa ba, amma ba wai bangar siyasa ba. Idan kuma ana yi to ya kamata ta tsawarta.
Tufafi
Na fi sha’awar tufafinmu na Arewa, kuma a wasu lokuta saboda zafi, nakan sa zannuwa masu huji (raga), nakan sa atamfa da shadda da kuma hijabi don na fito a cikin martaba da mutunci.