✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Hauwa Yalwa Sa Abubakar T/balewa: Ilimi sinadarin zaman duniya ne

Hajiya Hauwa Yalwa Tafawa balewa ‘yar marigayi Firayi Minista Sa Abubakar Tafawa balewa ta 12 ce. Ta fara karatun yaki da jahilci har ta kammala…

Hajiya Hauwa Yalwa Sa Abubakar T/BalewaHajiya Hauwa Yalwa Tafawa balewa ‘yar marigayi Firayi Minista Sa Abubakar Tafawa balewa ta 12 ce. Ta fara karatun yaki da jahilci har ta kammala jami’a. A yanzu ita ce Babbar Daraktar Hukumar Ilmin Manya a Jihar Bauchi. Ta shawarci jama’a su nemi ilimi domin shi ne sinadarin zaman duniya.

Tarihin Rayuwata
An haife ni a  garin Bauchi a ranar 12 ga watan Disamba, 1959. Sunan mahaifiyata Hajiya A’ishatu Jummai, ita ce matar mahaifina ta biyu, har yanzu tana raye, na yi gwagwarmayar karatu inda na fara daga makarantar firamare ta Shekal, bayan rasuwar mahaifinmu sai na koma makarantar Yalwa Practicing School wacce lokacin Turawa ne ke rike da ita. Ina aji biyar zan shiga shida sai aka cire ni aka yi mini aure ina shekara 14, sai muka tafi da maigidana Dokta Bala Mohammed zuwa Amurka bayan na haifi dana na farko a can sai ya sanya ni a makarantar  koyon Turanci na tsawon wata tara lokacin yana karatun digirinsa na uku  kan nazarin siyasa (political science). Mun  zauna a Ohio da Washington DC. Bayan mun dawo Najeriya sai na ce zan koma makaranta.
A Lokacin na haifi ’yata sai na koma WTC  Kano a shekarar  1979, amma da suka ji turancina sai suka yi  mini jarrabawa na shiga aji biyu. A lokacin sai na sake samun ciki na uku a aji hudu na sake barin makarantar, sai bayan na haihu na koma wata makaranta da ake kira SAS. Bayan shekara biyar sai na koma Bauchi don kammala jarrabawar sakandare da a baya ban samu na yi ba, amma da na ga ba zai yi wu ba sai na shiga makarantar yaki da Jahilci ta Adult and Non Formal Education a Bauchi.  Na fara daga ajin farko, sai na yi rijistar jarrabawar Pribate GCE, aka yi jarrabawa ta yi kyau na kawo. Na rubuta kasidar farko a karamar Hukumar Bauchi inda na yi aikin gwaji wato Project, daga nan sai suka ba ni aiki na Organiza ta yaki da jahilci lokacin da Hajiya Mairiga dangikka ta yi ritaya ba kuma wacce take da irin wannan takarda sai ni don haka aka ba ni. Daga nan sai na nemi tafiya karatu jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya sashen ilmin manya na yi Difloma. Bayan shekara biyu na koma Jami’ar Maiduguri na yi digiri a 1988 duk a kan ilmin manya.
Burina ina karama
Gaskiya ba ni da burin aikin yaki da jahilci tun ina karama, burina shi ne na yi karatun likita, amma Allah bai kaddara ba sai na zama likitar yakar jahilci. Ina wannan aiki sai na ji an bude sashin ilmin manya na kasa  sai na ga suna neman aiki a jarida sai na nema  aka dauke ni na fara aiki da su. Muka ci gaba da wayar da kan jama’a game da ci gaban zamani  da koyar da sana’a kan wannan na gina rayuwata. Kuma a yanzu haka na bude makarantu, a gidanmu akwai makarantar da mahaifina ya bude tun shekarar 1948 ni nake lura da ita, don shi yake koyar da iyayenmu mata yaki da jahilci a lokacin.
Nasabata da Naja’atu Mohammed
Mun hada miji, amma ba mu zauna a gida daya mun san juna ba, sai bayan rasuwar mijinmu.
Tarbiyya da mahaifinmu ya ba mu
Ina da shekara shida aka kashe mahaifinmu, amma na samu kyakkyawar tarbiyya a wurinsa har lokacin da iyayenmu mata da sauran yayyu suka dora a kan wacce ya ba mu. Akwai bambancin tarbiyya a da da yanzu musamman ganin a lokacin shi ne Firayi Minista amma da ’ya’yan kowa muke karatu, kuma haka idan ya zo hutu yakan dauke mu mu tafi gona mu zauna a yi aikin gona tare da shi. Mahaifinmu ya bi gida-gida yana kwaso yara yana hadawa da nasa yana kai wa ya tsaya sai ya ga an yi rijistar dukkan yaran da ya shiga ya fito da su kafin ya bar makarantar.
Yanayin tsaron mahaifinmu
Gaskiya ba mu san wani tsaro a tsakaninmu da shi da jama’a kamar yadda ake tsanantawa a yanzu ba, idan za mu zo Bauchi daga Legas tare yake dauko mu a jirgi zuwa filin jirgin saman Bauchi. Kuma haka mahaifanmu mata har mamaki suke yi yadda ake turo masu tsaro sai ya ce su tafi. Ko a cikin gidansa akwai ‘yan doka da ‘yan sanda, idan ya ga sun matsa masa sai ya ce su tafi su yi hidimominsu a bar shi ya gana da jama’a haka yake fita a cikin garin Bauchi ya je zumunci da kafarsa yake yawo da abokansa da ‘yan uwa daga gidanmu a Kofar Ran har fada ba tare da wasu jami’an tsaro ba. Ina tunawa idan ya dauki hutu daga Legas yakan zo Bauchi sai ya wuce kauye inda tushensa yake wato Kafin Madaki, a can yake zuwa ya yi hutunsa har ya gama a cikin wasu ‘yan bukkoki. Haka mu ma iyali sai a kwashe mu a mota mu tafi can mu zauna tare da shi har ya gama hutu yana ziyartar abokansa irin su Turakin Jama’are, Allah Ya ji kansu. Kuma ya fi yin hutunsa a cikin damina don lura da gonarsa da ke Kafin Madaki.

Dangantakarmu da Kafin Madaki da Tafawa balewa
Gaskiya ya samu Tafawa balewa ne daga sama, amma asalinsa dan Kafin Madaki ne,  zumunci  ya kai shi can, don kakansa Filata Borno ne, da mahaifiyarsa da Babansa suka zo Kafin Madaki. Sai mahaifinsa ya rasu, mahaifiyarsa  ta zauna a cikin Gerawan Kafin Madaki a Zala, da uban ya rasu sai ta auri  wani Bageri a wajen suka raini mahaifinmu sunansa Yakubu dan Zala, mahaifin Yakubun kuma sunansa Isa. Ajiyan Bauchi Attahiru, idan ya zo Zala ba wanda yake so sai babanmu. Mamar Yakubu ta bar Zala ta dawo Turum ta yi aure, sarkin Turum ya so Yakubun sosai. A wannan lokaci da Ajiya Attahiru ya ga mahaifinmu sai ya tambaya dan wane ne aka ce masa maraya ne sai ya ce yana son sa ya matsa ya dauke shi ya tafi da shi inda yake Sarauta a Tafawa balewa. Amma shi kansa babanmu a Bauchi aka haife shi. A lokacin da za su zo makarantar Middle School a Bauchi daga Elimentare ta Tafawa balewa akwai Madakin Bauchi shi ma Garba Yakubu ne, sai sunansu ya zo daya, don haka aka bambanta sunayen  aji aka karawa mahaifinmu Tafawa balewa inda ya samo wannan suna ke nan.  
kalubalen Rayuwa
Bai wuce gwagwarmayar  karatu ba, na kama nan ya zille na kama can ya kubce amma ban gaji ba sai na sake tashi tsaye da haka har na yi karfi na gama digiri, na koma zan yi digiri na biyu a Kano sai ya gagara. Sai na koma na yi babbar Diflomar kwarewa kan harkokin gudanarwa (PGDM). Kuma na zauna a   ofishin shiyya na hukumar yaki da jahilci ta kasa a Bauchi, daga can aka dawo da ni wannan ofis na zama babbar Darakta.
Shawarata ga mata
Rayuwar yau sai da hakuri da jan hankalin yara, a nuna musu kada su rika hangen abin da ya fi karfinsu.
Tallafi daga maigidana
Dukkan mazajen da na aura sun rasu, amma kamar Kilishin Bauchi, Marigayi Alhaji Adamu Yusuf lokacin da muka zauna mun yi rayuwa mai inganci da ya rasu mutane sun tausaya mini sosai, saboda zaman tsakani da Allah da muka yi da tarbiyyar ’ya’yanmu duk ya zamo abin koyi ga mutane game da yadda muka zauna da juna. Shi ma Dokta Bala Mohammed mun yi zaman arziki kuma duk na samu tallafi da goyon baya daga gare su.
Nasiha ga al’umma
A nemi ilmi a kuma ilmantar da yara tare da ba su tarbiyya ta kwarai don sauke nauyin da Allah ya dora mana, a hada  ilmin addini da na zamani, Ilimin gishirin zaman duniya ne. Allah Ya umarci manzonSa har zuwa kan mu, maza da mata babba da yaro kowa ya tashi ya nemi ilmi sai rayuwarsa ta zama akwai bambanci da ta jahili.
Tufafi da abinci
Na fi son ganye da abincin gargajiya, sutura kuma na fi son ta Hausawa da ta Musulunci.
Kira game da siyasa
Hakika siyasa ta haife mu kuma mutane sun ba ni shawarar na shiga  siyasa, don haka nake kira kowa ya tsaya kan gaskiya kada ya bari a cuce shi, ba zan fitar da tsammanin siyasa ba amma ba ni da ra’ayi, ban san idan ta zama siyasar jihadi a jawo ni dole an dasa ba.