✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Fati Larai Abubakar: Na shiga siyasa don in sanya al’umma farin ciki

  Hajiya Fati Larai Abubakar, tsohuwar ‘yar Majalisar Dokokin Jihar Neja ce, wadda ta wakilci mazabar Chanchaga, a yanzu kuma Mai Ba Gwamnan Jihar Neja,…

 

Hajiya Fati Larai Abubakar, tsohuwar ‘yar Majalisar Dokokin Jihar Neja ce, wadda ta wakilci mazabar Chanchaga, a yanzu kuma Mai Ba Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu Shawara a Kan Al’amuran Mata. Ta nemi a rika ba ilimin mata mahimmanci. Ta ce ta shiga siyasa don ta sanya al’umma farin ciki.

 

Tarihin rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Fati Larai Abubakar, ‘yar siyasa ce a karamar Hukumar Chanchaga. An haife ni a Bidda, Jihar Neja. Mahaifina shi ne marigayi Alhaji Abubakar Ladan Usman, mahaifiyata kuwa Hajiya Fatima Usman. Mu 18 a wurin mahaifinmu wanda Allah Ya yi wa rasuwa fiye da shekara 10. Allah Ya yi masa rahama.
Na yi firamare ta Sabon gida da ke Bidda, sannan na yi sakandare a makarantar Maryama wadda a yanzu ake kira ‘Gobernment Girls Secondary School Bida’. Na yi karatun share fagen shiga jami’a a Kwalejin Ilimi Mai Zurfi da ke Zungeru (Zungeru College Of Adbanced Studies). Daga nan na yi karatun ilimin Malanta a Kwalejin Ilimi da ke Minna wadda a can baya aka fi sani da A.T.C. Bayan nan sai na yi kwas din Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Abuja.
Ban fuskanci wani muhimmin kalubale ba yayin da nake neman ilimi domin mahaifina mutum ne mai saukin kai, wanda ya san muhimmancin ilimi.Ya yarda a ba kowa hakkinsa daidai gwargwado. Dukkanmu ‘ya’yansa mata ya sa mun yi karatu ba kamar yadda aka yi ta fama da wasu a wancan lokacin ba. Abu daya ne ya tsana daga wurinmu shi ne, yawon banza. Da muka fahimci haka sai muka kiyaye.
Haduwata da mata ‘yan siyasa
Ban tsinci wannan al’amarin da na samu kai na a ciki da rana tsaka ba. Dalilina kuwa shi ne, na bude ido na ga mahaifina yana ciki gadan-gadan. Babban abin sha’awa fa lokacin da nake maka magana ba mu girma ba, mun san ya yi ta hidindimu da jama’a har ta kai ga ya nemi kujerar Majalisar Tarayya, Allah Bai ba shi nasara ba. Huldar da ya yi ta yi da jama’a na daga cikin muhimman abubuwan da suka ba ni sha’awa, sannan ga shi na nazarci siyasa a Jami’a, ina kuma yinta. Na kuma roki Allah Ya cika mini burina in zama ‘yar siyasa yayin da nake karama.
A lokacin da muke tasowa mukan ziyarci marigayiya Hajiya Gambo Sawaba, wadda a duk lokacin da muka je takan ba mu tarihin rayuwarta, daga lokacin da take karama har ta kai ga matsayin da ta samu kanta. Wadannan abubuwan da muka ji daga wurinta sun ba ni sha’awa da kuma kara mini kaimin son yin siyasa. Ka ga a yau in dai za ka bayyana siyasar kasar nan dole ka sako ta a ciki. Bayan ita, mun ziyarci marigayiya Hajiya Laila Dogon Yaro inda a nan ma na kara daukar wasu darussan da suka hada da: kowa yana iya harkar siyasa yadda ya kamata. Wadannan sun taimaka mini wurin daukar darussa sosai wadanda na yi amfani da su na samu nasara.
Akwai bambanci tsakanin siyasar da muke yi da wadda aka koya mana a aji. Akasarin wadanda suke siyasar da muka samu kanmu a wannan kasar, ba karanta ta suka yi ba, sun shige ta ne kawai, idan ka ce za ka kawo salon wadda aka koya maka a aji za ka samu sabani kwarai da gaske.Wannan siyasar da muke a zahirance makarantar kanta ce, wadda ta saba da wadda aka koya mana wadanda suka fi mayar da hankali ga tarihin siyasar da rawar da magabata suka taka. Idan ka kwantar da hankali za ka iya hada biyun wuri daya ka samu biyan bukata. Na shiga siyasa don sanya al’umma farin ciki.
Ra’ayina game da ilimin mata
Ba wani abu ne ke hana iyaye sa ‘ya’yansu musamman mata a makaranta ba sai jahilci. Kada ka manta Allah (SWT) Ya umurce mu da mu san Shi kafin mu bauta maSa. Manzon Allah (SAW) ya ce neman ilimi dole ne a kan kowane Musulmi, wato na addini da kuma na sana’a, wanda a nan ilimin zamani wato na boko ya shigo ciki ke nan, ko da kuwa a kasar Sin za a same shi. A yau idan ba ka da ilimi, tasirinka a cikin al’umma ragagge ne. Wasu iyayen da suka ki barin ‘ya’yansu mata su yi ilimin daga baya sun yi da-na-sanin daukar wannan matakin, saboda sun ga irin hasken da ke tattare da samun ilimin ba kadan ba ne. Iyaye ba su da hujjar hana ‘ya’yansu neman ilimin nan, ga makarantu nan ko’ina duk irin wadda kake so. A daina dora wa yara talla. Talla tana da matukar illa inda ta nan ne akan yi wa wasu fyade da sauran munanan ayyuka.

kungiyoyi
Al’amarin kungiyoyi na da muhimmancin gaske a rayuwar kowace al’umma. kasashe da dama wadanda suka ci gaba sun samu nasara ta hanyar bunkasa ayyukan kungiyoyi wadanda suka karkata ta inganta rayuwar al’umma. Ina da kungiyar da ake kira Farin Wata Multi Purpose Society da wadansu wadanda muka assasa muna gudanar da ayyukan da muka tsara a fannoni daban-daban don samun biyan bukata.
Nasarori
A nan, ba abin da zan ce sai godiya ga Allah SWT da Ya yi mini jagora, sai kuma Gwamnan Jihar Neja Babangida Aliyu wanda ya ba ni damar yi masa aiki a matsayi mai ba shi shawara a kan al’amuran mata.
Na bullo da tsarin shiga iri daya ta farin gyale a duk lokacin da za mu fita zuwa wuraren da aka gayyace mu. Wannan ya taimaka mana matuka a duk lokacin da aka yi wani abin da bai dace ba, muna saurin gane wadda ta yi ko a cikin mu take ko a’a. Idan a cikin mu take sai mu ja mata kunne.
Ba tarurrukan gwamnati kadai muke zuwa ba. Muna haduwa a lokacin da wata daga cikin wadannan matan ta samu wani abin farin ciki, sai mu je mu taya ta murna, mu kuma yi mata addu’o’i a kan wannan abin da ta karu da shi. Hakan ya sa wadannan mutanen suka zama tamkar uwa daya uba daya, ka ga wannan babban abin alfahari ne.
Farin cikina
Matan wannan Jihar sun ga bambanci daga lokacin da wannan Gwamnati ta Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ta hau karagar mulki zuwa yau, don kuwa sun samu kulawa yadda ta kamata. Lokaci zuwa lokaci mukan gudanar da taron wayar wa juna kai game da yadda za mu taimaka a fahimtar da jama’a manufofin gwamnati da yadda za su ci moriyarta gwargwadon hali. Wannan ya sanya ni farin ciki.
kasashen da na ziyarta
Bari mu fara da nan Najeriya, babu jihar da ban je ba. Na taba zama Shugabar Mata ta kasa ta ‘Turaki banguard’ wanda wannan ya sa muka zaga da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar muka yi ta kamfe daga wannan jihar zuwa wancan a hankali har muka gama. Ka ga dama ta farko ke nan, wadda ta ba mu damar mu’amala da jama’a daban-daban. Sai kuma kasashen ketare. Na ziyarci Saudiyya da Sudan da Ingila da Afrika Ta Kudu da Dubai da Senegal da sauransu.
Abinci
Ka san ni Banufiya ce don haka na fi sha’awar tuwon shinkafa da miyar wake, sannan doya busa, haka kuma shinkafa dafa duka, da danginta. Idan ka zo bangaren miya, na fi son duk miyar da aka yi ta da ganye da dage-dage. Dangane da abin sha kuwa na fi son fura da nono da zobo da duk abubuwan shan da aka yi da citta.
Tufafi
A wannan fannin na fi son atamfa sai gambari da kuma leshi.
Fatana
Ina fatan in gama da duniya lafiya, in kuma ci gaba da tasiri a rayuwar jama’a. Babban abin da nake son jama’a su gane shi ne, ba dole sai kana da kudi sosai ne za ka iya tasiri a rayuwar jama’a ba, akwai hanyoyi da yawa wadanda za ka iya yin hakan, babban abin koyin mu Annabi Muhammad (SAW) ya nuna a wasu daga cikin hadisansa shi ne ayyukan alheri masu yawa ciki har da kawar da abin da ka ga zai cuci wani daga kan hanya kamar kusa ko kaya da dangoginsu sadakoki ne.