✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya A’isha Tanko Yakasai: Mata a guji zaman banza

Hajiya A’isha Tanko Yakasai ’yar fitaccen dan siyasa Tanko Yakasai ce. Ita ce Babbar Darakta a Kamfanin Satco Nigeria Limited da kuma na A-Tee Klean…

Hajiya A’isha Tanko Yakasai ’yar fitaccen dan siyasa Tanko Yakasai ce. Ita ce Babbar Darakta a Kamfanin Satco Nigeria Limited da kuma na A-Tee Klean Limited. Ta yi bayanin yadda take gwagwarmayar siyasa da kuma tabbatar da ’yancin mata. Ta bukaci mata su guji zaman banza.

Tarihin rayuwata
Assalamu alaikum, sunana A’isha Tanko Yakasai. An haife ni a Kano, na yi dukkan karatuna a Kano. Ina gudanar da harkokin kasuwancina a Kano, ni ce Babbar Daraktar Kamfanin Satco Nigeria Limited da kuma na A-Tee Klean Limited.
Abin da ba zan manta da shi lokacin da nake karama ba
Nakan tuna irin zaman da na yi da ’yan uwana lokacin da nake karama, ina da kusaci da mahaifana, ina son dukkan ’yan uwana. Irin rayuwar da muka yi a lokacin idan na tuna sai na ji farin ciki ya lullube ni. Mahaifa da ’yan uwana su ne kashin baya, su ne ginshikina a kan duk wani matsayi da na taka. Yanzu ba ma tare kasancewar kowa ya yi aure, saduwa ta yi wahala.  
Mutanen da nake koyi da su
Kowa yana da wadanda yake kwaikwayo, musamman ma wadanda suka ba da gudunmuwa wajen yin ayyukan da ke bunkusa kasa ko suke taimakon jama’a. A cikin irin wadannan mutanen akwai Mai Shari’a Maryam Aloma Mukhtar. Mace mai hazaka da kuma mayar da hankali wajen gudanar da dukkan ayyukanta.  Ta fita da matakin digiri mai daraja ta daya a jami’a, kuma ita ce babbar lauya ta farko daga Arewacin Najeriya. Alkali mace ta farko a Babbar Kotu a Jihar Kano. Mace ta farko mai shari’a a Kotun daukaka kara ta kasa, mace ta farko mai shari’a a Babbar Kotun kasa da sauran mukaman da ta rike.  Bayan ita sai Sanata Daisy danjuma, gudunmuwar da take bayarwa a bangaren siyasa da kuma kare hakkin mata da kuma gwagwarmaya wajen tabbatar da ’yancin mata. Daga nan sai Ministar Kudi, Ngozi Okonjo-Iwela da matar Mataimakin shugaban kasa Hajiya Amina Namadi Sambo.
Abin da nake so a rika tuna ni da shi
Ina so a rika tuna ni a matsayin wacce ta taimaka wa masu karamin karfi. Zan ci gaba da taimaka wa jama’a matukar ina raye. Ba za a bar komai a hannun gwamnati ba, domin ba za ta iya yin komai ba. A fahimta jama’a na fama da talauci, mutane da yawa ba sa iya cin abinci sau uku a rana. Ballantana a rika batun yadda za su magance matsalolin da suka shafi rashin lafiya da muhalli da sauransu. Don haka ya zama dole mu taimaka don saukaka abubuwa. Yin hakan wani alkawari ne da na dauka wa kaina, na kuma yi hakan ne don rayuwata ta zama ta sadaukarwa wajen inganta rayuwar jama’a.
kalubale
Na fuskanci kalubale, dole in kasance tare da ’ya’yana, ni nake shirya su su tafi makaranta. Ba kuma kawai su je makaranta ba, nakan bi diddigin yadda suke karatu. Nakan halarci dukkan bukukuwan makaratunsu, nakan yi hakan ne don in kasance wani jigo a bangaren rayuwarsu. Baya ga haka ga ayyukan gida. Na ji dadin yadda mijina yake da saurin fahimta, hakan ya taimaka mini wajen shawo kan dukkan abin da ya ci mini tuwo a kwarya.  
Yadda nake lura da kaina
Ina  yin abubuwa biyu da suke kara mayar da ni mai karancin shekaru. Da farko nakan tabbata na kwanta barci da wuri, don na samu isasshen barci. Na biyu ba na bari damuwa ta addabe ni har ta hana ni rawar gaban hantsi. Ko yaya damuwa take ba na bari ta yi tasiri wajen nakasar da walwala da farin cikina, domin na tabbata a kowane tsanani akwai sauki. Shi ya sa masu iya magana suke cewa babu amfani a yi kuka idan madara ta zube, domin kukan ba zai magance komai ba.
Yadda nake hutawa
Hutawa wani abu ne da kowane dan Adam yake bukata.  Zaman lafiya a gidana shi ne babban sinadarin da ke samar mini da hutu. Duk da halin da ake ciki a kasar nan, idan ina gida nakan dan ji natsuwa da kwanciyar hankali. Idan ’ya’yana suna surutu sai in tafi dakina.
kasashen da nake zuwa hutu
Zan iya cewa Ingila, saboda ina da ’yan uwa da suke zama a can- dan uwa da kuma ‘yar uwa da kuma wadansu daga cikin ’yan uwan kishiyar mahaifiyata. Nakan ziyarce su lokaci zuwa lokaci. Sai kuma birnin Faris, a kasar Faransa, ina son birnin ne saboda yanayinsa, inda jama’a daga sassan duniya suke ziyartarsa. Za ka hadu da jama’a masu yawa. Akwai wuraren da za ka ziyarta ka samu natsuwa a birnin.

Abinci
Na fi son abincinmu na Najeriya, ba na sha’awar abincin Turawa. Idan kana so ka burge ni to ka ba ni tuwo miyar busasshen karkashi ko sakwara da miyar egushi ko tuwon semo da miyar Ogbono. Ina da yakinin abincinmu ya fi na Turawa inganci da kara lafiya da kuma dandano mai gamsarwa.
Salon sanya tufafi
Ba na daga cikin mutanen da suka dauki duniya da fadi, nakan yi komai a saukake. Ba na yin kwalliya don nuna ni wata ce, ko kuma in rika dagawa. Ga bangaren kayan kwalliya da tufafi ba na daukar duniya da fadi.
Yadda na hadu da mijina
Ba kowa ne yake iya tunawa ba. Na hadu da mijina ne wata rana na je gidan wata kawata. A lokacin mijin nawa shi ne likitansu. Cikin ikon Allah na je gidan shi ma ya zo don ya yi aikinsa. Na gode wa Allah da Ya sanya ya a zama mijina. Ya taimaka mini sosai wajen cim ma burina a rayuwa.
Gwagwarmayar rayuwa
Ayyaukan yau da kullum su ne gwagwarmayar rayuwa. Jama’a sukan yi tsammanin ba ni da matsala, wanda kuma ba haka ba ne, kowane dan Adam yana da matsalar da ke damunsa. Ni ma na fuskanci matsaloli kamar kowane dan Adam, sai dai abin da nake da tabbaci shi ne a kowane tsanani akwai sauki. Ba na taba bari a gane ina da damuwa, shanye ta nake yi. Jama’a sukan yi mini ganin wacce ba ta da matsala kuma ina jin dadin hakan, domin  na samu tabbacin shanye damuwar da nake yi tana aiki.
Abin da ba zan manta da shi ba
Mutuwar kanwata Maryam Tanko Yakasai. Na yi bakin ciki sosai. Allah Ya Gafarta mata da kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Gwagwarmayar siyasa
Ana shan gwagwarmayar siyasa, musamman ma a nan Abuja. Dole sai mutum ya kasance mai juriya da kuma kwazo. Ba zan daina ci gaba da gwagwarmayar siyasa har sai an samu ci gaba a Najeriya. Ba zan taba gajiya ba har sai rayuwar al’umma ta inganta. Alhamdulillahi ana samun ci gaba kadan-kadan.
Shawara ga mata
Ina ba mata shawara su hada kansu, su kuma samu wani abu da za su rika yi. Ya kamata mata su hada kai wajen ganin an biya musu bukatunsu a kasar nan. Ya kamata a inganta rayuwar mata ta bangaren sana’o’i, a samar musu gurbi a bangaren bunkasa tattalin arzikin kasa. A rika shawara da mata wajen ayyukan ci gaban kasa. Kodayake a wannan gwamnatin an ba mata dama, amma muna bukatar kari.