✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadimin Gwamnan Katsina ya rasu a taron daurin aure

A wurin daurin 'ya'yana ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da gaisawa da jama'a.

Sabon Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina kan harkokin tsaro da suka shafi yankin Daura, Alhaji Rabe Ibrahim Jibia ya riga mu gidan gaskiya.

Jibia ya yanke jiki ya fadi a babban masallacin Juma’a na Kumassie yayin halartar daurin auren ‘ya’yan mai ba wa gwamnan shawara kan harkoki a jihar, Alhaji Ibrahim Katsina.

Da yake tabbatar da faruwa lamarin, Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce, “tabbas a wurin daurin ‘ya’yana ne ya yanke jiki ya fadi yayin da yake gaisawa da mutane, inda aka dauke shi zuwa asibiti kuma a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.”

Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce marigayi Rabe, na daga cikin sabbin hadimai da Gwamna Masari ya nada kan harkokin da suka shafi tsaro a jihar.

Ya mika sakon ta’aziyyarsa a madadin gwamnan jihar ga iyalan mamacin da kuma daukacin abokan aikinsa baki daya.