A ranar Talatar makon da ya gabata, `ya`yar wannan jaridar, wato Daily Trust, a shafinta na 52, ta dauko wata talla da ke dauke da sa hannun Sakataren Kwamitin Amintattun mutane na Jam`iyyar PDP na kasa baki daya Sanata Walid Jibrin mai kanu kamar haka-“dan Sakataren Kwamitin Amintattu na Jam`iyyar PDP ya shiga CPC. Labarin da jaridar Leadership ta ranar Litinin din makon jiyan ta buga a shafinta na 11. Ga wanda ya san harkokin yada labarai, yasan, irin wannan kanun labarai da Jaridu da Mujallu da tashoshin Radiyo da Telebijin da sauransu, sukan buga ko su yada, akan kirasu “Fuska mai saida riga” a jaridance. Ma`ana a danganta wanda labari ya shafa da wani babban mutum, komai nisan nasabarsa da wani babban mutum, don kawai kiran kasuwa ga kafofin yada labaran, don haka ba wani sabon abu ba ne.
Irin wannan tsarin yada labarai ya faru tsakanin Sanata Walid Jibrin da jaridar Leadership ta waccan Litinin da na ambata a sama, (Sanata Walid dai dan uwa ne ga marigayi Guruf Kyaftin Usman Jibrin tsohon gwamnan mulkin soja na tsohuwar Jihar Kaduna a lokacin mulkin Murtala/Obasanjo 1975 zuwa 1979, lokacin da Obasanjon ya nemi ya rage karfin zangon tashar ta Kaduna aniyar da ta sa Guruf Kyaftin Jibrin ya ajiye kaki), Jaridar Leadeship, da wancan kanu da na ambata tun farko.
Daga dukkan alamu wancan labari bai yi wa Sanata Walid Jibrin dadi ba, akan irin yadda jaridar ta alakanta dan dan uwansa, wato Imrana Usman Jibrin da cewa dansa ne ya shiga jam`iyyar CPC a jihar Nassarawa, wadda ita ce jiharsa ta haihuwa, saboda kasancewar shi Sanata Walid Jibrin a yau yana rike da babban mikami a jam`iyyar PDP, Jam`iyyar da a yau Allah Ya ara mata mulkin kasar nan. Amma kuma Ni a ra`ayi na yadda Sanata Walid ya nuna bacin ransa, da yadda ya nemi ya nisanta kansa da dan danuwansa, sai nike ganin ya dauki abin da zafi, wanda zai iya shuka kiyayya da gaba ta din-din-din a cikin bushiyar da Alhaji Jibrin ya shuka.
Alal misali a waccan talla da Sanata Walid ya sanya a jaridar Daily Trust, ya fara da lissafin su `ya`yan Alhaji Jibrin su takwas ne maza da mata da suke da `ya`ya 61, sannan ya kara da cewa Imrana Usman Jibrin da ya shiga jam`iyyar CPC, dan marigayi Usman Jibrin ne, da ya rasu shekaru 2, da suka gabata, inda ya ce. “Duk da yake Imrana dan danuwa ne, amma ba ni da iko akansa, kamar yadda nike da shi akan kowane daga cikin `ya`yana 10,” in ji Sanata Walid. Ni abin da zan fara ce bai wuce in ce, Allah Ya jikan magabatanmu da rahamarSa irinsu Alhaji Jibrin, wadanda su a zamaninsu saboda tsananin zumunci da alkunya (wadanda koda a jahilce suka yi su, sun samu lada, sun kuma zauna lafiya da kowa da kowa, musamman zuriyarsu, sun kuma mutu har gobe muna masu addu`ar nema masu rahama).
A fadar Sanata Walid, wai Imrana, ya bari wasu shugabannin jam`iyyar CPC na jihar Nassarawa da ya ce idanuwansu sun rufe, wajen neman bata masa suna da mutunci, wadanda ya ce babban laifinsa ga irin wadancan abokan adawa, shi ne irin yadda ya iya rike kambin jam`iyyasu ta PDP tun daga mazabarsa zuwa karamar Hukumarsa zuwa jiha da gagarumin rinjaye. Ya ci gaba da cewa `yan adawar suna kuma nukura ne akan biyayyarsa ga shugaban kasa Jonathan da mataimakinsa. Anan sai ya tabbatarwa da duniya cewa shigar Imrana Usman Jbrin dan Usman Jibrin cikin siyasa, ba abin da zai kara gareshi da ya wuce kara jaddada imaninsa da goyon bayansa ga jam`iyyar PDP a Jihar Nassarawa da kasa baki daya.
Ga iyalen dan uwansa kuwa Sanata Walid, cewa ya yi “Zan ci gaba da girmama dan uwana marigayi Usman da matansa 4, da dukkan sauran `ya`yansa. Rashin biyayyar Imrana gare ni, ba za ta sa in taba canja ra`ayi na wajen kula da Iyalen marigayin ba. Dangantaka za ta ci gaba da kara karfafa ga dukkansu.”
Ba sai an fadi ba mai karatu, wannan hali da aka shiga tsakanin Sanata Walid Jibrin da iyalen dan uwansa marigayi Usman Jibrin zai bude wata kafa da za ta aza harsashin samun raunin danganta tsakanin iyalen biyu, koda kuwa sauran dangi ba su shiga ba. Mai karatu yi tunani, kai ka ce Imrana cewa ya yi ya bar Musulunci, da har danuwan mahaifinsa da a yau bai da mahaifi kamarsa zai fitar da kudi wuri na gugar wuri, har kusan Naira dubu 500 (N4677), ya sa talla a jarida yana nisanta kansa da shi. Ina ma wadancan kudaden ya yi amfani da su wajen sayen abinci da sutturu ya raba ga `yan uwan nasu, ko ya ba mabukata alfarmar wannan watan na Azumin watan Ramadan.
Jaridu su yi labari irin nasa, ba kansa farau ba,ina Sanata Walid yake lokacin da aka samu dan Alhaji Bamanga Tukur shugaban jam`iyyarsu ta PDP na kasa baki daya ana tuhumarsa da laifin yana cikin masu badakalar cuwa-cuwar kudaden sassaucin man fetur a bara, tuhumar da yanzu take kotu. Abinda kawai Alhaji Bamanga ya yi shine mayar da martini da jaridu suka buga masa kyauta, shi ne, dansa baligi ne da zai iya daukar dukkan abin da ya jajibo wa kansa, bisa ga harkokinsa na neman dari da kwabo da yake kai, daga nan ya samu lafiya. Haka kuma gobe in an samu wani dake da dangantaka ta kusa da wani babba a kasar nan a cikin wani hali da ya kamata jama`a su sani, za a alakantasa da babban mutum din.
Ya kamata Sanata Walid ya sa ni cewa matsayin da ya kai a cikin jam`iyyar PDP yanzu, ba ciki zai dauwama ba, amma zumunci tsakaninsa da `yan uwansa a cikinsa yake fatan ya dauwama, ba ma ya a cikin tsatsonsu idan a yau shi ne shugaba baki daya, don haka ya kamata ya rika cizawa, yana hurawa kafin ya dauki matsayi. Yau yana biyayya ga shugaba Jonatahan da mataimakinsa, don jam`iyyar PDP ta hadasu gobe kuma za ta iya kasance wani labarin daban. Don haka me ya yi zafi?
Haba Sanata Walid Jibril Me ya yi zafi haka?
A ranar Talatar makon da ya gabata, `ya`yar wannan jaridar, wato Daily Trust, a shafinta na 52, ta dauko wata talla da ke dauke da…