✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haba Janar T.Y. Xanjuma! MeHaba Janar T.Y. Danjuma! Me jiya ta yi ballantana yau? jiya ta yi ballantana yau?

A makon jiya ne aka ruwaito cewa su Janar TY Danjuma sun ce: “Gwamnatin Buhari ce silar rikice-rikicen da suke aukuwa a kasar nan.” Gaskiyar…

A makon jiya ne aka ruwaito cewa su Janar TY Danjuma sun ce: “Gwamnatin Buhari ce silar rikice-rikicen da suke aukuwa a kasar nan.” Gaskiyar magana ita ce, wadanda suka yi wadannan kalamai da suka kira kansu dattawan Kiristoci ga alamu sun fadi haka ne saboda an toshe hanyoyin da suke ci gaba da wawure dukiyar kasar nan a yanzu, kuma an fara gano bakin zaren masu haddasa rikice-rikicen addini da kabilanci domin cimma wata manufa ta siyasa. Da ma masu iya magana sun ce idan ruwa ya kare wa kifi, sai ya kare a wuta.

Rikice-rikicen da suka auku a Najeriya sun faro ne da rikicin Maitatsine a Kano, Maitatsine kuma ba dan Najeriya ba ne, ba Musulmi ba ne. Har yau ba a aiwatar da rahoton Mai shari’a Anyagulu ba kan rikicin Maitatsine. Farfesa Dauda Ojobi ya fadi tarihin Maitatsine kowa zai iya neman kaset din ko ta kafafen watsa labarai na zamani.

Sai rikicin Zangon Kataf da aka samu hannun Manjo Janar Zamani Lekwot (mai ritaya) a cikin wadanda suka haddasa shi. Mai Shari’a Karibi Whyte ya yanke wa Janar Zamani Lekwot hukuncin kisa kan hannunsa a rikicin na Zangon Kataf, amma Shugaban Kasa na lokacin ya hana a zartar masa da hukuncin kisan. Wai yau Zamani Lekwot ne don rashin kunya yake da bakin magana da karfin gwiwar zargin Shugaba Buhari da haddasa rikice-rikice!

Rikicin Boko Haram, an yi zargin akwai hannun wani tsohon Shugaban Sojojin Najeriya da wani tsohon Gwamnan Jihar Borno da wasu kasashen waje – kamar yadda wani Bature mai bincike da gwamnati ta gayyato daga Austreliya ya tabbatar. Duk wadannan sun faru ne a karkashin wadansu shugabanni ba Buhari ba. To me ya sa su Janar TY Danjuma ba su yi magana kan haka ba, sai su dora wa gwamnatin Buhari laifin barnar da ta zo ta iske kuma take kokarin magancewa? Ko so suke a ci gaba da tashe-tashen hankulan suna samun kwangiloli da haka?

A kasar nan fa ga sojoji da ’yan sanda, ga Kwastam da Imagereshin, ga SSS da NIA, da sauran hukumomin tsaro amma aka samu masu tada kayar baya suka rika kama garuruwa da kauyuka suna kafa tutarsu T.Y Danjuma da Zamani Lekwot suna nan ba su taba zargin Shugaban Kasar da aka rika samun wadannan matsalolin a karkashin mulkinsa ba, sai da Buhari ya kwato garuruwan da masu ta-da-kayar bayan suka mamaye, aka fara kwato kudaden da barayin shugabanni suka sace, aka fara kwato ’yan mata da mutanen da ’yan Boko Haram suka sace, za su ce wai gwamnatin ce ke haddasa haka.

Lokacin su Janar Ihejirika da Minima duk abubuwan da suka faru ba a ji bakin T.Y Danjuma da Zamani Lekwot ba sai yanzu, yanzun ma da suka ga Shugaba Buhari yana fama da rashin lafiya kuma ba su samu biyan bukatarsu ta kashin kansu a wurinsa ba, maimakon su tausaya masa, su yi masa fatan samun cikakkiyar lafiya – sai suka bige da bata shi saboda muguwar manufa suka fake da bambancin addini! Ba su taba bude baki sun zarga ko suka soki tsohon Shugaban Kasa Jonathan ba, duk da irin barna da zubar da jinin da aka tafka a lokacin mulkinsa.

Maganar su T.Y Danjuma cewa ana son musuluntar da Najeriya ya kamata su fahimci Shari’ar Musulunci an kebe ta ce domin Musulmi, kuma Musulmi suna yada addininsu ne ba tare da jiran gwamnati ta taimaka musu ba. Idan masu da’awar bin Linjila ko Attaura ko Zabura sun gurbata littattafansu sun ki yin aiki da su, to mu Musulmi da Allah Ya tsare wa Alkur’ani babu mai iya gurba ta shi, za mu ci gaba da aiki da koyarwarsa. Kuma Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa kowa ’yancin yin addinin da yake so, don haka bai kamata su rika tsangwamar Musulmin Najeriya a kan addininmu na Musulunci. Wa ya hana su yada nasu addinin? Wane Musulmi ne ya taba cewa kada Kiristoci su yi aiki da littafinsu ko dokokin addininsu? Duk wata doka da ta yi karo da ta Allah to kamata ya yi Musulmin gaskiya da Kiristan gaskiya su ce ba su yarda da ita ba. Ba wai a rika karya da kazafin wani yana son musuluntar da kasa ba. Babu wanda ya isa ya yi mana barazana a kan sai mun fifita dokar da masu shan giya, su ci mushe, su ci kare da doki ko jaki, masu bugar da matasa da ababen sa maye, a kan dokar Allah Madaukaki don kawai a cimma wata manufa ta siyasa.

Da ma mu, mun gane Muhammadu Buhari shi kadai ya zama daban a cikin sojojin da suka yi mulki, saboda haka duk masu ja da ikon Allah, ga su ga Allah wanda ba Ya mutuwa ko rashin lafiya, ba Ya neman komai a wurin kowa, Shi ne kowa yake neman komai a wurinSa, Shi ne Mai kowa Mai komai, Mai bayar da mulki ga wanda Ya so, Ya kwace daga hannun wanda Ya so a duk lokacin da Ya so. Duk wadansu tsofaffin sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati da suka daka warwaso a  kan rijiyoyin man fetur da kadarorin gwamnati suka sace arzikin kasarmu, talakawan da aka yi wa illa ta hanyar yi musu sata sun ishe su, ga kuma mala’ikun Allah wadanda babu wani mai tasiri a kansu sai Allah da Ya halicce su, suke aiki da umarninSa, ba fasa wa ballantana kuskure a kan umarnin da Ya yi musu.

Mun ja layi tsakanin mu (masu kaya) da barayin shugabanni, sanin haka ne ya sa suke so su yi amfani da addini su bata a rubibi, to sun makara. Mun gaji da shugabancin wakilan wasu kasashe makiyanmu, masu son rusa mana kasa su sace mana arzikin kasarmu ta haihuwa iyaye da kakanni.

Ko masu mulkin gado idan suka kauce wa Allah, suka shiga tsafi da fajirci da sata, za mu kauce musu, ballantana sojoji masu kwatar mulki da bindiga ko farar hula masu magudin zabe da suka yi mana sata har da satar doka da cushe a kasafin kudi, suka hada kai da matsafa wadanda suka wawashe mana arzikin kasa, suka rabe rijiyoyin manmu a tsakanin junansu, wadannan mutane sun wadanda Shugaba Muhammadu Buhari yake kokarin bi mana kadinsu a yanzu, makiya Allah makiya bayin Allah suka sa masa kahon zuka. To duk wanda ya taba Muhammadu Buhari, mu ya taba, mu da aka yi wa sata da kwace da kisa. Saboda haka ga mu, ga su, ga Allah – Gatan mara gata!

A lokacin mulkin soja aka fara samun wani Shugaban Kasa ya bai wa kansa rijiyoyin mai, ya bai wa ’yan uwansa sojoji, ciki har da Janar T.Y Danjuma da sarakuna rijiyoyin man, maimakon ’yan kasuwa da suka cancanta. Buhari har yanzu bai mallaki rijiya ko rijiyoyin mai ba, balle ya bai wa wadansu sojojin ko dattawan giri. Matatun mai na Najeriya ba Muhammadu Buhari ne ya rusa su ba!

Jeffrey Robinson (Ba’amurke) da ya rubuta a littafinsa mai suna “THE SINK,” ya bayyana karara cewa: “Daga cikin Dala biliyan 120 da aka sace daga Najeriya, aka fitar da su wasu kasashe – akwai zargin Janar Ibrahim Babangida kai-tsaye a matsayin Shugaban Kasa daga 1985-1993, ya mallaki Dala biliyan 20 daga ciki. Kuma wasu majiyoyi na duniya sun bayyana adadin dukiyar da ya wawura daga baitul malin Najeriya zuwa sama da Dala biliyan 35.”

Dole a binciki wannan zargin a kuma kwato wa ’yan Najeriya dukiyarsu idan har hakan ta tabbata. Ina  Dala biliyan 12.2 na rarar mai na Yakin Tekun Fasha?  Ina kudaden da ake zargin Janar Abacha da iyalansa da wawashewa? Ina kudaden ajiya na kasar waje da ake zargin Janar Abdussalami Abubakar sun kwasa? Ina kudaden badakalar Halliburton?  Ina kudaden da Obasanjo ya kwato, amma ya ki mai da su aljihun gwamnati?  Ina Dala biliyan 20 billion daga cikin Dala biliyan 49.8 na danyen mai da ba a shigar CBN ba a lokacin Jonathan?

Wadannan kadan ne daga cikin barna da badakala da shugabanni suka yi a baya – wadanda suka jefa Najeriya a mugun halin da take ciki a yanzu. Kuma Shugaba Buhari ya fara kwato biliyoyin da aka sace, yana kokarin inganta harkokin mulki da shari’a yadda za a hukunta kowane mai laifi, a yi adalci ba sani ba sabo. Amma ana ta yi masa sharri da tadiye masa kafa da sunan addini ko bangaranci da kabilanci. Babu wani addini da ya yarda shugabanni su yi sata da kisa a kyale su. Dukkanmu Allah ne Ya halicce mu ba barayin shugabanni ba. Yunkurin da wasu kasashe suka yi wajen taimaka mana don a kwato mana dukiyar kasarmu da barayin shugabanni suka sace, suka jibge a wasu kasashe, taimako ne daga Allah, ba daga wani mutum ba.